Babu wani yankin Najeriya da ke karkashin ikon yan ta’adda, inji Buratai

Babu wani yankin Najeriya da ke karkashin ikon yan ta’adda, inji Buratai

Shugaban rundunar sojin Najeriya Lafatanal Janar Tukur Buratai, a jiya Talata, 10 ga watan Satumba, ya bayyana cewa hukumar sojin ta musanta zargin cewa yan ta'addan Boko Haram da kungiyar ISWAP, na a kowani yanki na kasar.

Buratai ya kuma bayyana cewa tura dakarun sojin da aka yi domin ayyukan cikin gida goyon baya ne ga yan sanda a matsayinta na hukumar tsaro da ke kan gaba.

Yayin da yake magana a Abuja a wani taro mai taken: "Terrorism, Insurgency and Incidence of Electoral Violence in Nigeria: Role of Security Agencuiarees,” wacce kungiyar NEPAD tare da cibiyar rundunar suka shirya, Buratai yace rundunar soji ta bayyana muhimman cigaba da aka samu wajen kare rayuka da dukiyoyi, musamman a yankin Arewa maso gabas inda tayi musun cewa yan ta’addan sun kafa sansani.

Matsayar shugaban sojin ya bambanta da na gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zullum, da wasu kauyuka a jihar wadanda suka soki dabaran rundunar sojin Najeriya na kafa manyan sansani wanda hakan yasa suka cire tsammani da rundunar sojin.

Rundunar sojin ta kuma yi watsi da ikirarin, inda tace ta yantar da kananan hukumomi 22 na jihar tun 2015.

KU KARANTA KUMA: Takaicin duniya ya sa wani dan shekara 27 rataye kansa a Kano

Yace an dauki matakin ne domin tabbatar da dorewar aminci da yarda tsakanin mutane da kuma martabar rundunar sojin Najeriya.

Shugaban sojin yace an kashe jami'ai da sojoji da dama sannan za a ci gaba da kashe su duk don kare kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel