An kama Sojojin da aka tura yakin Boko Haram ya na fashi a Garin Yola

An kama Sojojin da aka tura yakin Boko Haram ya na fashi a Garin Yola

Wani Soja da ke kan aiki ya shiga hannun hukuma da zargin yi wa wata mata fashi da makami. A halin da ake ciki, an tura wannan Soja ne zuwa aikin yaki da ‘yan ta’addan Boko Haram a kasar.

Kamar yadda mu ka samu labari, wannan Sojan Najeriya da ya kamata ace yana bakin daga a Garin Munguno domin ganin bayan ‘yan ta’adda, ya bude ne da tare mutane a cikin mota a jihar Adamawa.

Bayan gabatar da wannan Soja da wani mutumi da ake zargi da fashi a Garin Yola, Kakakin ‘yan sanda na jihar Adamawa, DSP Sulaiman Nguroje, ya ce sun aikata laifin ne a Ranar Talata da tsakar dare.

Sulaiman Nguroje ya sanar da Duniya cewa ana zargin wadannan mutane da tsare wata hanya a Garin Yola da kimanin karfe 1:00 na dare. A nan ne su ka tare wata mata su ka yi mata fashi a kan titi.

DSP Nguroje yake cewa ‘yan fashin sun tare wata Baiwar Allah ne inda su ka tursasa ta har ta mika motarta. Jami’in ‘yan sandan ya bayyana kirar motar a matsayin Toyota Camry kamar yadda mu ka ji.

KU KARANTA: Wani Matashi ya rataye kansa har lahira a Garin Kano

“An yi dace wani Jami’in ‘yan sanda da ke aiki a lokacin ya kai kara, inda nan take aka shiga aiki, tare da hadin kan ‘yan banga, an kama mutanen da ake zargi da aikata wannan mugun aikin.” Inji Nguroje.

Kakakin ya ce: “Mun iya karbo motar, da kuma bindigar AK-47 da casbi 35 na harsashi daga ‘yan fashin. Bayan tambayoyi, an gano cewa Dampa Hyellambamun, Soja ne wanda aka tura aiki a Monguno.”

Sojan ya ce: “Na samu damar fita zuwa Yola, wanda ya kamata ace na koma tun 10 ga Agusta.” Da aka tambaye sa abin da ya sa ya ke fashi, sai ya ce ya zai yi an mika masa bindiga babu albashi ko alawus?

Jami’in Sojan ya ce yunwa ce ta rutsa sa har ta kai yana neman ya ci babu. ‘Yan sanda sun bayyana cewa za su mika wadanda aka kaman a kotu domin a yanke masu hukunci da zarar sun gama bincike.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Newspaper

Online view pixel