An tsane ni, an rada min sunan batanci 'Okoro Hausa' duk saboda APC - Okorocha

An tsane ni, an rada min sunan batanci 'Okoro Hausa' duk saboda APC - Okorocha

Tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha ya koka kan abinda ya kira 'cin mutunci' da jam'iyyarsa ta All Progressives Congress, APC ke masa duk da irin sadaukarwa da hidima na kudi da ya yi mata.

Sanatan mai wakiltan mazabar Imo West ya shaidawa manema labarai a ranar Talata a Abuja cewa an saka masa da 'sharri' a APC saboda irin hidimar da ya yi wa jam'iyyar musamman a yankin Kudu maso Gabas.

Ya ce dole ya yi hannun riga da wasu 'yan uwansa da abokan siyasa domin ya tabbatar jam'iyyar ta kafu da kafarta a Kudu maso Gabas amma sakayarsa da aka yi masa mai ban mamaki itace dakatar da shi.

Okorocha ya ce, "Idan ba ku manta ba, an yi ta kira na da sunayen batanci kamar 'Okoro Hausa' da kuma cewa ina gina masallatai da sauransu.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Kotu ta kwace kujerar dan majalisar APC a jihar Kano

"Amma duk nayi watsi da hakan domin nayi imanin cewa ina yi wa al'umma ta abinda ya dace ne.

"Ina daga cikin wadanda suka taka muhimmiyar rawa don ganin Oshiomhole ya zama shugaban jam'iyya kuma ba zai iya musanta hakan ba.

"Na nayi gwagwarmaya da APC a Kudu maso Gabas amma yanzu na ga APC tana son hada kai da Gwamna Emeka Ihedioha idan zai muzanta Rochas.

"Wannan abin takaici ne kuma ya kashe min jiki domin tsamanni na shine dukkan mu 'yan uwa ne da ke aiki don ganin cigaban kasar nan.

"Amma yadda abubuwa ke tafi ba bu alamar wani maslaha. Kuma kowa ya yi shiru kan batun.

"Ban ma san matsayin dakatar da ni da aka yi ba. Saboda cikin 'yan kwanakin nan ban san me ke faruwa a jam'iyyar APC ba.

"Amma yadda na ga kowa ya yi shiru, hakan na nufin ba wani matsala bane.

"Yanzu ina jira ne kuma ina tunanin abinda zan yi a gaba amma har yanzu ni dan jam'iyyar APC ne kuma ina kaunar jam'iyyar kuma zan mara mata baya."

Okorocha ya kara da cewa kimar Shugaba Muhammadu Buhari ne ke rike da APC tare da cewa yankin Arewa ce kan gaba a siyasar Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel