Kola Balogun ya doke Ajimobi wajen shari’ar kujerar Sanatan Oyo

Kola Balogun ya doke Ajimobi wajen shari’ar kujerar Sanatan Oyo

Kotun da ke karbar korafi game da zabukan majalisar tarayya da jiha a Oyo ta yanke hukunci game da karar da Abiola Ajimobi ya kai yana kalubalantar zaben Sanatan PDP Kola Balogun.

Hukumar dillacin labarai ta rahoto cewa kotu ta tabbatar da nasarar Kola Balogun na jam’iyyar PDP a matsayin zababben Sanatan jihar Oyo ta Kudu a zaben da aka yi a farkon shekarar nan.

Alkalai sun ba Sanata Kola Balogun gaskiya a shari’ar da tsohon gwamna Abiola Ajimobi ya shigar bayan zabe. Alkalai uku a karkashin jagorancin Anthony Akpovi su ka yanke hukunci.

Sauran masu shari’ar su ne Sambo Daka da Chinyere Ani wanda su ka gamsu cewa PDP ta ci zabe. Sanata Balogun ya samu kuri’u 105,720 a zaben ne wanda Ajimobi ya tashi da kuri’u 92,218.

Mai shari’a Akpovi ya karanto hukuncin da aka yi inda ya ce shaidun da mai gabatar da kara ya gabatar duk masu tattara sakamakon zaben Mazabu ne don haka ba su ya kamata a saurara ba.

KU KARANTA: Ana rigima tsakanin PDP da APC yayin da Kotu za ta yi zaman karshe

Shugaban zaman ya kuma bayyana cewa ‘dan takarar APC da ya shigar da kara gaban kuliya ya gaza nuna inda PDP ta ki amfani da na’urar aikin zabe ko kuma ta sabawa ka'idar tantance masu kada kuri’a.

Babban Alkalin da ya saurari wannan kara da Abiola Ajimobi ya shigar kan ‘dan takarar jam'iyyar PDP ya ce mafi yawan shaidun da APC su ka yi amfani da su domin a rusa zaben ba su da alaka da shari'ar.

Budu da kari Anthony Akpovi yace shaidun da Ajimobi ya gabatar a kotu sun buge ne da labaran soki-burutsu don haka kotu ta ce bai iya gamsar da ita a kan abin da zai sa a soke zaben na Fubrairun ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel