Mutum daya ya rasa ransa, wasu kuma sun sami rauni a zanga-zangar da dalibai suka yi

Mutum daya ya rasa ransa, wasu kuma sun sami rauni a zanga-zangar da dalibai suka yi

- Wani dalibi da ke shekarar farko a jami'ar tarayya da ke Oye Ekiti ya rasa ransa yayin zanga-zanga

- Daliban sunyi zanga-zangar ne akan rashin wutar lantarki da ke addabarsu

- Harbin 'yan sanda masu kwantar da tarzomar ne ya samu dalibin inda ya mutu har lahira

Dalibin shekarar farko a jami'ar tarayya da ke Oye Ekiti, Oluwaseyi Kehinde, ya mutu har lahira yayin da 'yan sanda suka yi harbi don kwantar da zanga-zanga da daliban jami'ar suka yi.

Wasu daliban kuwa raunika suka samu yayin zanga-zanga kan rashin wutar lantarki da daliban suka yi a ranar Talata.

Mun samu rahoton cewa, an hari uwargidan gwamnan jihar Ekiti yayin zanga-zangar.

Dalibai da yawa daga jami'ar sun sanar da majiyarmu cewa harin da aka kaiwa tawagar uwargidan gwamnan shi yasa 'yan sanda maida mummunan martani.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa daliban masu zanga-zanga sun tare hanyar uwargidan gwamnan yayin da take dawowa daga zagayen kananan hukumomi 16 na jihar.

KU KARANTA: Sowore: Anyi musayar yawu tsakanin lauya da mai shari'a

"Yayin da aka tare uwargidan gwamnan, wani jami'in Dan sanda wanda suke tare da tawagar ya sauka tare da marin shugaban kungiyar daliban," wani ganau ya sanar mana.

"A yunkurin dalibai na maida martani ga Dan sandan, sai hargitsi ya tashi."

"Yan sandan sun gano kangarewar masu zanga-zangar ne don haka suka fara harbe-harbe. An tabbatar da rasuwar wani dalibin shekarar farko inda mutane uku ke kwance a gadon asibiti. Wasu kuma sun samu raunika," wani dalibi ya sanar mana.

Idan da ace yan sanda ba su kara hargitsa lamarin ba, da qila zanga-zangar bata kai haka ba, inji wani dalibi.

A lokacin da aka tuntubi mai magana da yawun makarantar, Godfrey Bakri, ya sanar da Premium Times cewa baya cikin makarantar a don haka ba zai bada tabbacin mutuwar dalibin ba.

A zancen Hukumar yan sanda da suka sanar a ranar Talata, sun musanta cewa jami'ansu sunyi harbi a wajen zanga-zangar.

Mai magana da yawun 'yan sandan, Caleb Ikechukwu yace daliban da ke zanga-zangar sun bar harabar makarantarsu inda suka danganta har zuwa babban titin Oye-Ikole-Lokoja tare da rufesa. Yace hakan ya kawo rashin kwanciyar hankali da kuma rufe hanyar ababen hawa.

"Daliban masu zanga-zangar har ofishin rarrabe wutar lantarki ta Benin suka je da ke Oye Ekiti. 'Yan sandan da aka tura ne suka hanzarta kawo karshen barnar da suka fara a ofishin."

"'Yan sandan ne suka tarwatsa taron sannan suka cire shingen da suka rufe titi da shi."

"Daliban masu zanga-zangar sai suka koma kan tawagar uwargidan gwamnan jihar. Sun dau doka a hannunsu ta hanyar kokarin lalata motocin tawagar. Sun kara da dukan 'yan sandan da suke wajen don kwantar da tarzoma."

"A yanzu dai ana cigaba da bincike kuma za a gurfanar da masu hannu a ciki don fuskantar fushin hukumar." Inji mai magana da yawun 'yan sandan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel