Tirkashi: Gwamnatin tarayya ta kwato N900bn da yan majalisar dokokin tarayya suka sace

Tirkashi: Gwamnatin tarayya ta kwato N900bn da yan majalisar dokokin tarayya suka sace

Babban sakataren kwamitin da ke ba shugaban kasa shawara akan yaki da rashawa, Farfesa Sadiq Radda, yace gwamnatin tarayya ta dawo da kimanin naira biliyan 900 na aikin mazaba daga wasu mambobi majalisar dokokin tarayya.

Radda ya fada ma manema labarai a gefen taron yaki da rashawa a 14 daa aka gudanar a Maiduguri, babban birnin jihar Borno cewa kudin an baiwa sanatoci da mambobin majalisar wakilai ne domin aiwatar da ayyuka a mazabunsu.

Sai dai ya nuna danasanin cewa wasu mambobin majalisar dokokin tarayyar sun sace kudaden amma cewa hukumar yaki da rashawa ta ICPC ta kwato kudaden.

Yace ICPC ta kuma kafa kwamiti akan tsaro. Yace kwamitin za ta bayyana duk gwamnan da ya lakume wadannan kudade da sunan tsaro. “Mutane za su yi bayani. Babu gwamnan da zai ci bulus ta hany fakewa da tsaro. Ya zama dole mutane suyi bayani,” inji shi.

KU KARANTA KUMA: Rana ba ta karya: Yau za'a yanke hukunci tsakanin Buhari da Atiku

Ya roki yan Najeriya da kada su amshi abunda ya kira ga makircin barayin mutane wadanda suka yi wa yaki da cin hanci da rashawar gwamnati lakabi da siyasa. Ya yi ikirarin cewa barayin mutane ba za su taba gani kowani alkhairi a abunda gwamnatin ke yi ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel