Dalilin da yasa na jefa dan cikina mai watanni 4 a rafi - Aliyu

Dalilin da yasa na jefa dan cikina mai watanni 4 a rafi - Aliyu

Rundunar tsaro na NSDC reshen jihar Niger ta kama wani matashi mai suna Mustapha Aliyu dan shekara 20, kan zargin kashe dansa mai watanni hudu a duniya.

Kwamandan NSDC, George U. Edem, a zantawa da yayi da manema labarai a ranar Talata, 10 ga watan Satumba, a Minna yace wanda ake zargin, wanda ya kasance dan achaba kuma dan asalin jihar Kebbi, amma yana zaune a Niger, ya jefar da yaron a rafin Oli da ke karamar hukumar Borgu a ranar 7 ga watan Satumba.

Kwamandan yace an kama mai laifin ne a ranar da ya aikata abun a garin Tamanai inda yake da zama, biyo bayan tsegumi da aka samu daga mazauna kauyen.

Yace wanda ake zargin ya amsa laifinsa, sannan cewa rundunar za ta mika shi ga yan sanda domin a hukunta shi.

Kwamandan yace har yanzu ba a gano gawar yaron daga cikin rafin ba bayan an sha neman sa.

Wanda ake zargin a hira da yayi da Crime Trust a hedkwatar NSDC, yace ya kashe dan nasa ne saboda bai san yadda zai yi dashi ba.

A cewarsa, iyayensa basu ji dadi ba saboda an haifi yaron ne ba ta hanyar aure ba kuma sun ki amsar sa.

KU KARANTA KUMA: Hukumar EFCC ta cika hannu da yan Yahoo-yahoo 13, ta kama manyan motoci 5

“Mahaifiyata bata ji dadi ba tun daga lokacin da ta samu labarin cewa budurwata na da juna biyu. Abubuwa sun dada tabarbarewa ne a lokacin da ta haihu, mahaifiyata tace lallai babu abunda za tayi da shege.

“A wannan ranar, lokacin da na ziyarci yarinyar, sai mahaifiyarta tace lallai sai na karbi dana tunda iyayena sun ki yarda ayi shirin aure,” inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel