Kotun zabe: ‘Yan Atiku da Buhari sun kidime da rikici a kafafen sadarwa

Kotun zabe: ‘Yan Atiku da Buhari sun kidime da rikici a kafafen sadarwa

Magoya bayan ‘dan takarar PDP a zaben 2019, Atiku Abubakar da kuma Mabiya shugaban kasa Muhammadu Buhari su na ta cacar baki na tsawon lokaci yayin da kotu za ta yi zaman karshe.

Mabiya manyan ‘yan siyasar su na faman rikici a shafukansu na sada zumunta na Tuwita ne a daidai lokacin da ake jira kotun da ke sauraron karar zaben 2019 ya yanke hukunci a yau Laraba.

‘Yan ganin kashe-nin Atiku su na ta yada sakonni da taken #AtikuIsComing, ma’ana su na sa rai kotu ta rushe nasarar da shugaban kasa Buhari da APC su ka samu a zaben da aka yi bana.

Sakonni masu kunshe da lagon na #AtikuIsComing sun kai kusan 5000 a farkon makon nan. Haka zalika su ma Mabiya shugaba Buhari sun dage da na su shirin na #AtikuIsNotComing.

A daidai lokacin da ake ta faman cacar bakin, Reno Omokri wanda ya taba aiki a matsayin Mai ba tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan shawara ya nemi Buhari ya kyale kotu su yi aikinsu.

KU KARANTA:

Atiku ya na kalubalantar nasarar da shugaban kasa Buhari ya samu a zaben 2019 inda ya fadawa kotu cewa APC ba ta da kuri’un halas din lashe zabe, sannan kuma ‘dan takararta ya yi coge.

Lauyoyin Alhaji Atiku Abubakar sun hakikance a kan cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari bai da takardun karatun da za su ba shi damar tsayawa takara. Buhari ya karyata wannan zargi.

Ga kadan daga cikin irin ce-ce-ku-cen da ake yi tsakanin Magoya bayan ‘yan takarar nan bana:

Wasu na ganin cewa Atiku Abubakar zai sha kunya an jima a kotu.

M Abba gani yake yi yau Atiku zai samu nasara a gaban kuliya.

Adjogbe Tejiri ya na da ra'ayin cewa shari'ar Atiku ba za ta kai ko ina ba.

Mista Nelson ya fito ya na cewa, babu Atiku babu kayansa.

Shi ma wani Bawan Allah ya ce da kamar wuya kotu ta ba Atiku nasara

Ga abin da Paul Flurry yake fada:

Wani Lauya kuma ya yi kaca-kaca ne da wani da ke marawa Atiku baya

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel