Musayan fursunoni: Yayinda gwamnatin Katsina ta saki yan bindiga 6, su kuma sun saki mutane 20 sa suka sace

Musayan fursunoni: Yayinda gwamnatin Katsina ta saki yan bindiga 6, su kuma sun saki mutane 20 sa suka sace

- A jiya Talata ne jami'an tsaro a jihar Katsina suka saki 'yan ta'adda 6 da ke hannunsu

- Hakan ya biyo bayan umarnin da gwamnatin jihar ta baiwa jami'an tsaron

- Gwamnatin jihar ta ce hakan na daga cikin yarjejeniyarta da 'yan ta'addan don samun sakin wadanda suka yi garkuwa da su

Jami'an tsaron jihar Katsina sun saki 'yan ta'adda 6 bayan umarnin Gwamnatin jihar. Gwamnatin tayi haka ne bayan tattaunawar wanzar da zaman lafiya da tayi da 'yan ta'addan da suka addabi kananan hukumomi 8 na jihar.

Kamfanin illancin labarai ta ruwaito cewa kananan hukumomin Dandume, Sabuwa, Faskari, Kankara, Safana, Danmusa, Batsari da Jibiya na jihar Katsina sun dade a cikin matsalolin da 'yan ta'addan suka jefasu.

Halin da suke ciki ne yasa gwamnatin jihar ta kirkiro hanyar tattaunawar da shuwagabannin 'yan ta'addan a makon da ya gabata. A hakan ne suka yi yarjejeniyar da ta kunshi sakin wasu daga cikin 'yan ta'addan da ke hannun jami'an tsaro.

KU KARANTA: Sowore: Anyi musayar yawu tsakanin lauya da mai shari'a

Gwamnan jihar, Aminu Masari ya tunatar yayi mika 'yan ta'addan, cewa shi da shuwagabannin jami'an tsaro kusan sati daya kenan suka dauka suna ziyartar kananan hukumomin da ke da iyaka da dajin Rugu, wanda ya zama maboya ga 'yan ta'addan.

Masari yayi bayanin cewa, daga cikin yarjejeniyarsu ne mika 'yan ta'addan da ke hannun jami'an tsaro ga 'yan uwansu.

Kamar yadda yace, 'yan ta'addan zasu bada mutanen da suka yi garkuwa dasu ga gwamnatin.

Yace sun fara aiwatar da yarjejeniyar ne a ranar litinin din nan inda 'yan ta'addan suka saki mutane biyar kuma zasu kara sakin mutane 20 kafin.

Ya kara da cewa za a kara sakin wasu wadanda aka yi garkuwa da su din duk a cikin yarjejeniyar zaman lafiya da aka yi dasu.

Masari ya tabbatar da cewa za a kammala sakin mutanen a cikin kwana daya zuwa biyu ta yadda gwamnatin jihar zata fara aiwatar da kashi na biyu ta yarjejeniyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel