Rana ba ta karya: Yau za'a yanke hukunci tsakanin Buhari da Atiku

Rana ba ta karya: Yau za'a yanke hukunci tsakanin Buhari da Atiku

Kotun zaben shugaban kasa a yau zata yanke hukunci kan karar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da dan takararta, Atiku Abubakar, inda suke kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa na 23 ga Febrairu, 2019.

A ranar Talata, diraktan yada labaran kotun daukaka kara, Sa'adatu Musa, ta bayyana hakan a jawabin da ta gabatar.

Atiku da PDP na kalubalantar hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta INEC kan alanta Buhari matsayin wanda ya lashe zabe da kuri'u 15,191,846 sabanin nasu 11,262,978.

A ranar 18 ga Maris, PDP ta gabatar da bukatarta na farko ga kotu inda ta bukaci hukumar INEC ta bata daman binciken akwatunan zaben da akayi amfani da su lokacin zabe.

KU KARANTA: Na hallaka yayana saboda marowaci ne, ya fiye bukulu - Matashi

Amma hukumar INEC, Buhari da APC sun nuna rashin amincewarsu da wannan bukata, daga karshe, an basu dama.

Ana cikin wannan dambarwa, jam'iyyar PDP da Atiku suka bukaci shugabar kotun, Zainab Bulkachuwa, ta janye daga zama a kotun saboda maigidanta dan jam'iyyar APC ne.

Bayan makonni uku, Zainab Bulkachuwa, ta janye daga karar kuma aka maye gurbinta da Alkali Garba.

Babban abinda PDP da Atiku suka dogara da shi shine cewa shugaba Buhari ya yiwa kotu karyan cewa kwalin karatun sakandarensa na hannun hukumar Soji alhalin kotun ta musanta hakan.

A tsawon kwanaki 178 da akayi ana zaman kotu, PDP ta gabatar da shaidu 62, takardun hujjoji 50,000. Wasu daga cikin shaidun PDP sune tsohon aminin Buhari, Buba Galadima.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel