Najeriya ta na sa ran kashe Tiriliyan 9.78 a shekara mai zuwa Inji Ahmed

Najeriya ta na sa ran kashe Tiriliyan 9.78 a shekara mai zuwa Inji Ahmed

Mun samu labari cewa gwamnatin tarayya ta shirya kashe fiye da Naira tiriliyan 9 a shekarar 2020. Ministar kudi da tattalin arzikin Najeriya, Zainab Ahmed, ta bayyana wannan a makon nan.

Zainab Ahmed ta sanar da jama’a cewa gwamnatin Najeriya ta na hararo kasafin kudin Naira tiriliyan 9.78 a shekarar da za a shiga. Ministar ta bayyana wannan ne jiya Talata a Garin Abuja.

A wajen wani taro da aka shirya domin kaddamar da shirin matsakaicin tsarin tattalin arzikin Najeriya na shekarar 2010 zuwa 2022, Ahmed ta bayyana cewa kasafin kudin Najeriya zai ragu.

A shekarar bana, an yi kasafin Naira tiriliyan 10.06, amma wannan karo za a shirya kasafin Naira tiriliyan 9.78. Hakan na nufin abin da gwamnati ta ke son kashewa zai ragu da Biliyan 360.

Har ila yau, Ahmed ta koka da matsalar da ake samu wajen dabbaka shirin tattalin musamman wajen samun kudin shiga a Najeriya ganin yadda kudin da ake kashewa kan albashi ke karuwa.

Ministar kasar ta ce an tsara kasafin kudin na 2020 a kan farashin gangar man fetur a Dala 55 ne. Ana kuma haasashen cewa a duk rana Najeriya za ta hako danyen mai adadin ganga miliyan 2.18.

KU KARANTA: Shugaba Buhari zai karbe Biliyan 614 da ya ba Gwamnoni aro

Abin da wannan ke nufi shi ne gwamnatin Najeriya ta rage buri wajen lissafin abin da za ta samu daga man fetur. An bana, an yi hasashen za a saida ganguna danyen mai miliyan 2.3 a Dala 60.

Daga cikin wannan kasafi na Tiriliyan 9.7, za a warewa masu cin gashin kan su Naira Biliyan 526. Najeriya za ta kashe Tiriliyan 2.45 wajen biyan bashi, sannan albashi za su ci kusan Tiriliyan 4.7.

A shekarar da za a shiga, gwamnati ta na sa ran kashe Tiriliyan 2.05 ne wajen manyan ayyuka. A shekarar nan ta 2019, abin da aka ware a kundin kasafin kudi domin ayyuka ya haura Tiriliyan 3.

Game da yadda za a tatso wannan kudi, Ministar ta ce Tiriliyan 2.36 za su fito ne daga saida mai, sannan fiye da Tiriliyan 1.6 daga haraji da kason NLNG sai Biliyan 200 daga kudin da ke hannun barayi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel