Hukumar EFCC ta cika hannu da yan Yahoo-yahoo 13, ta kama manyan motoci 5

Hukumar EFCC ta cika hannu da yan Yahoo-yahoo 13, ta kama manyan motoci 5

Jami’an hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC sun daka wawa a wani katafaren gida inda gungun matasa masu damfara ta yanar gizo suke gudanar da mummunar aikinsu a jahar Enugu.

Legit.ng ta ruwaito EFCC ta bayyana nasarar kama wadannan matasa su 13 ne a shafinta na kafar sadarwar zamani ta Facebook, inda jami’anta sun kama matasan ne a wani gida dake Lomalinda, unguwar Marylanda na jahar Enugu.

KU KARANTA: Yan Boko Haram sun kashe mutane 3 a Borno, sun kwashe abinci da tumaki

Matasa yan damfarar da aka kama sun hada da: Frank Ikechukwu,Bright Alozie,Aloysious Ani, Ikenna Kingsley,Prince Ofoeze, David Ugonna,Prinewill Onyia,Chibuike Ebulue, Charles Chinedu,Christopher Patrick,Emeka Joel,Valentino Simon da Joseph Ani.

EFCC tace ta gudanar da samame a kan matasan ne bayan samu bayani dake nuna irin rayuwar da suke yi ta kashe kudi da almubazzaranci sakamakon ayyukan da suke yin a damfarar mutane ta amfani da shafukan yanar gizo.

Daga cikin abubuwan da EFCC ta kwato daga wajensu akwai wayoyin hannu, na’urar tafi da gidanka, katin ATM, motoci guda 5 da suka hada da; Honda Accord Salon, Lexus ES350 guda 3, da Mercedez Benz C300.

A wani labarin kuma, gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta tara kudaden shiga da suka kai naira tiriliyan 2 a cikin watanni 6 kacal, daga watan Janairu zuwa watan Yuni na shekarar 2019.

Daraktan ofishin kasafin kudi a fadar shugaban kasa, Ben Akabueze ne ya bayyana haka yayin da yake gabatar da jawabi game da tsare tsaren kashe kudi na gwamnatin tarayya na matsakaici zango a Abuja.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel