Mutane 2,200 sun amfana da tallafin hukumar NEMA a mahaifar shugaba Buhari

Mutane 2,200 sun amfana da tallafin hukumar NEMA a mahaifar shugaba Buhari

Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa, NEMA ta tallafawa akalla mutane 2,200 da suka gamu da ibtila’in ambaliyan ruwa a mahaifar shugaban kasa Muhammadu Buhari, garin Daura, ta jahar Katsina, inji rahoton NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito akalla ba’a kasara ba mutane 3,500 ne ambaliyan ruwan ya shafa a sakamakon wani ruwa kamar da bakin kwarya da aka tafka a garin na kusan sa’o’i 14 a garin Daura.

KU KARANTA: Yan Boko Haram sun kashe mutane 3 a Borno, sun kwashe abinci da tumaki

Shugaban aikin rarraba kayayyakin tallafin, Alhaji Aminu Nadari ya bayyana cewa dukkanin mutanen da ambaliyan ya shafa sun samu kayan tallafin da suka haka hada da buhunan shinkafa, wake, masara, barguna, katifu, man girki, kwanukan rufi, silip da kuma tabarmai.

Alhaji Nadari ya bayyana cewa sun gudanar da aikin rabon kayan tallafin yadda ya kamata, ta yadda suke duba iya barnar da ruwan ya yi ma mutum, iya adadin kayan tallafin da zai samu.

Ya kara da cewa akwai ragowar mutane 800 da kayan jin kan basu kai garesu ba, amma ya bada tabbacin suna jiran isowar wasu tireloli guda 2 dake kan hanya, kuma da zarar sun iso za su raba musu nasu kayayyakin.

Daga karshe Nadari ya yi kira ga wadanda suka samu tallafin dasu yi amfani dasu ta yadda ya kamata, kuma yace hukumar ba za ta lamunci cin dunduniya ba. Ita ma wata da ta samu tallafin, Hajiya Halima, wanda ta rasa dakuna 3 a sanadiyyar ambaliyan ta bayyana godiyarta ga hukumar NEMA.

Daga cikin kayan da NEMA ta rabar akawai buhunan shinkafa 300, na masara 300, na wake ma 300, buhunan siminti 1,200, bandir 500 na kwanukan rufi, pakitin kusa gua 100, tabarmai 500, silip 750, katifu 500, barguna 500 da kuma jarakunan mai 100.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Online view pixel