A Satumban nan Gwamnatin Tarayya za ta fara zaftare bashin da ta ba Jihohi – Ministar kudi

A Satumban nan Gwamnatin Tarayya za ta fara zaftare bashin da ta ba Jihohi – Ministar kudi

Daga karshen Watan Satumban 2019 ne gwamnatin tarayyar Najeriya za ta soma zare kudinta da ta ba wasu gwamnonin jihohi bashi a shekarar 2016 bayan sun gaza biyan albashin ma’aikata.

Hukumar dillacin labarai na kasa, NAN ta rahoto cewa gwamnatin Buhari za ta cire Naira biliyan 614 daga asusun wadannan gwamnoni sa su ka karbi aron kudi a hannun gwamnatin tarayya.

Gwamnati ta tsara yadda za a biya wannan kudi ta yadda kason da jihohi ke samu ba zai yi kasa ba sosai. Ministar kudi da tattalin arziki, Zainab Ahmed, ta bayyana wannan a jiya Ranar Talata.

A Ranar 10 ga Watan Satumba, 2019, Ahmed ta sanar da Manema labarai cewa za a soma zaftare wannan kudi ne daga cikin asusun FAAC da ake kason kudin tsakanin gwamnatoci a kasar.

Ministar ta yi wannan bayani ne lokacin da ta yi wani jawabi a kan matsakaicin tsarin tattalin arzikin Najeriya a babban birnin tarayya Abuja. Ta ce dama can aron kudin aka ba Jihohin.

KU KARANTA: Ma’aikata su na cikin wani hali bayan dage taron karin albashi a Najeriya

Ahmed ta ce: “Bashi ne babban bankin Najeriya ya tsaya gaba a ka ba wadannan jihohin, kuma za a maidawa CBN din wannan kudi daga ara. Saboda haka za mu rika maida kudin ne daga kason FAAC”

Za mu fara cire wannan kudi daga kason nan da za a yi. Amma, za mu duba halin tattalin arzikin da ake ciki. Mu na so jihohi su tsaya cikin karfin tattali, amma wannan ba sharadi ne biyan bashin ba.”

Babban banki na CBN ya ba jihohi 35 aron a kan ribar ruwa na 9%. Ma’aikatar kudi ce ta raba wannan kudi da amincewa da kuma sa hannun fadar shugaban kasa domin biyan albashi a lokacin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel