JNPSNC: Kai-komo bai kare ba bayan an daga zaman da aka shirya game da karin albashi

JNPSNC: Kai-komo bai kare ba bayan an daga zaman da aka shirya game da karin albashi

An dakatar da zaman da za ayi domin cigaba da tattaunawar da aka saba game da batun karin albashin ma’aikata a Najeriya. Mun samu labari cewa an dage wani zama da aka shirya zuwa gaba.

A ka’ida ya kamata ace gwamnatin tarayya ta zauna da kwamitin nan na JNPSNC wanda ke kokarin ganin an cin ma matsaya wajen dabbaka sabon mafi karancin albashin ma’aikata a Najeriya.

Yanzu rahoto ya zo mana daga hukumar dillacin labarai na kasa cewa an dage wannan zama da aka shirya tun 4 ga Satumba zuwa Ranar 16 ga Watan. Hakan na nufin sai a cikin farkon gobe za a zauna.

Alade Lawal wanda shi ne Sakataren wannan kwamiti na JNPSNC ya tabbatar da dage taron da aka shirya da gwamnatin Najeriya. Har yanzu dai ana ta je ka – ka dawo game da maganar karin albashin.

KU KARANTA: Kungiyar Kiristocin Najeriya sun jinjinawa Shugaba Buhari

Sakataren wannan kwamiti ya bayyana matakin dakatar da taron ne a Legas, Ranar Talata, 10 ga Watan Satumba, 2019. Lawal ya ce za su zauna da shugaban kasa Muhammadu Buhari a Litinin.

‘Yan kwadago su na ta samun matsala da gwamnati game da gazawar ta wajen dabbaka sabon tsarin mafi karancin albashin da aka kawo wanda tun a cikin Afrilun bana aka sa wa hannu.

JNPSNC na wakiltar kungiyoyin kwadagon kasar ne wajen ganin an cin ma yarjejeniyar yadda za a kasa sabon tsarin albashin ma’aikata. Kawo yanzu kwamitin bai iya cin ma wata matsaya ba.

Shugaban kungiyar NLC, Ayuba Wabba, ya ce su na tare da JNPSN a kan duk matsayar da ta dauka. An yi baram-baram ne a kan yadda za a dabbaka sabon albashin ga manyan ma’aikata.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel