An tsinci gawar wata yarinya a wani yankin dake garin Jos

An tsinci gawar wata yarinya a wani yankin dake garin Jos

-Al'ummar unguwar Gigiring sun ga abin al'ajabi yayin da suka wayi gari da gawar yarinya a yankin nasu

-Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Filato ya tabbatarwa manema labarai da aukuwar wannan lamari kuma ya ce ana kan yin bincike

Al’umma mazauna shiyyar Gigiring dake Jos babban birnin jihar Filato sun tashi jiya Talata inda suka ci karo da gawar wata yarinya an kashe ta kuma an jefar a saman layin dogo dake bayan kwalejin fasaha da kere-kere ta jihar.

Majiyar Daily Trust ta ruwaito cewa wata mata wadda ke zaune a unguwa, Mrs Egbo ta yi kira ga gwamnati da ta sanya fitilu a bisa titunan unguwar domin kawo karshen irin wannan mugun aiki.

KU KARANTA:Sojojin Najeriya na kama yara kanana da sunan Boko Haram – Kungiyar Human Right

Kakakin rundunar ‘yan sanda jihar Filato, Tyopev Terna ya tabbatar mana da aukuwar wannan lamari inda ya ce ana kan gudanar da bincike a kansa.

A wani labarin mai kama da wannan kuwa zaku ji cewa, Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Right Watch ta ce rundunar sojin Najeriya na kama yara kanana da sunan Boko Haram.

Kungiyar ta fadi wadannan maganganun ne cikin wani jawabi da ta wallafa mai shafuka hamsin, inda take zargin rundunar sojin da muzgunawa yara kanana ba tare da bin tsarin Majalisar dinkin duniya ba.

Kungiyar ta kara da cewa abu mafi dacewa shi ne idan har da gaske ne yaran masu laifi ne me zai hana a gurfanar da su a gaban shari’a, wanda shi ne abinda ya kamata ayi amma ba muzgunawa a garesu ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel