Tashin hankali: An kashe daliban jami'a guda biyu, bayan sun kaiwa matar gwamnan APC hari

Tashin hankali: An kashe daliban jami'a guda biyu, bayan sun kaiwa matar gwamnan APC hari

- Matar gwamnan jihar Ekiti ta sha da kyar bayan, dalibai da 'yan daba sun kaiwa tawagar ta hari

- Hakan ya biyo bayan wata zanga-zanga da daliban jami'ar tarayya ta jihar suke yi akan rashin wuta da suke fama da shi

- Daliban sun fito sun tare babbar hanyar da matar gwamnan za ta wuce ne, inda dakyar aka samu aka fita da ita daga wajen

Wata zanga-zanga da daliban jami'ar tarayya ta Ekiti suka yi jiya Talata 10 ga watan Satumba, ta zama rikici, yayin da suka kaiwa tawagar matar gwamnan jihar, Bisi Adeleye-Fayemi hari.

Daliban da suke zanga-zanga akan rashin wuta a makarantar ta su, an zarge su da tare babbar hanyar Oye-Ikole zuwa Abuja domin hana tawagar matar gwamnan wucewa, wacce ta dawo daga yawon bude ido a cikin kananan hukumomin jihar.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa 'yan daba da 'yan acaba ne suka shiga cikin daliban inda suka dinga jifan motocin matar gwamnan a lokacin da ta iso wajen. Wani wanda abin ya faru akan idonsa ya bayyana cewa wannan rikici yayi sanadiyyar mutuwar dalibai guda biyu, inda aka kone motoci sannan kuma aka kwace bindigogin jami'an tsaron da suke tare da matar gwamnan guda biyu.

KU KARANTA: Tirkashi: Wasu 'yan majalisu sun bawa hammata iska a cikin coci akan kujerar mulki

An ruwaito cewa an samu an fita da matar gwamnan daga wajen ne dakyar, inda sauran mutanen da suke tawagar suka nemi hanyar su.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Mr. Caleb Ikechukwu ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa an kaiwa matar gwamnan harin, amma kuma ya karyata jita-jitar mutuwar dalibai biyun da aka bayyana a rikicin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel