Zaben Sanata: Kotu ta yi watsi da karar tsohon gwamnan APC

Zaben Sanata: Kotu ta yi watsi da karar tsohon gwamnan APC

Kotun zaben majalisar dokoki na jiha da tarayya da ke zama a jihar Oyo, a ranar Talata, 10 ga watan Satumba, ta jaddada nasarar Sanata Kola Balogun na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), a zaben sanata mai wakiltan Oyo ta Kudu da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairu.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa tsohon gwamnan jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi, ya kalubalanci kaddamar da Balogun da INEC tayi a matsayin wanda ya lashe zaben.

NAN ta kuma ruwaito cewa Balogun ya samu kuri’u 105,720 wajen kayar da Ajimobi wanda ya samu kuri’u 92,218.

Kwamitin mutum uku na kotun zaben karkashin jagorancin Justis Anthony Akpovi, da Justis Sambo Daka da Justis Chinyere Ani a matsayin mambobi, sun tabbatar da nasarar Balogun.

Da Akpovi ke karanto hukuncin, ya bayyana cewa mafi akasarin shaidun da mai karar ya gabatar domin tabbatar da sakamakon rumfunar zaben sun kasance jami’an zabe na unguwanni ba wai mutanen da ya kamata su shaidi sakamakon ba.

KU KARANTA KUMA: Kotun zaben shugaban kasa: Mun tabbatar da yin nasara - APC

Ya bayyana cewa mafi akasarin shaidun da mai karar ya kira basu da amfani sannan cewa duk jawabinsu akan jita-jita ne.

Akpovi yace mai karar ya gaza tabbatar da dukkanin zarge-zargensa fiye da tsammani.

Don haka shugaban kotun zaben, ya soke karar Ajimobi sannan ya jaddada nasarar zaben Balogun, bayan ya samu yawan kiri’un da ake bukata, sannan ya kaddamar dashi a matsayin wanda ya lashe zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel