Hanyar lafiya: Mabiya Shi'a a Kano sun yi zamansu a gidajensu

Hanyar lafiya: Mabiya Shi'a a Kano sun yi zamansu a gidajensu

Mabiya kungiyar IMN (Islamic Movement of Nigeria), wacce aka fi kira da Shi'a, sun yi zamansu a gidajensu a jihar Kano sabanini ikirarinsu na fito wa domin gudanar da tattakin ranar Ashoura a jihar.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa an ga wasu tsirarun mabiya Shi'ar na taru wa a unguwar Kurnar Asabe, amma da suka hango jami'an 'yan sanda na tunkaro su sai suka tarwatse a guje.

Unguwar Kurnar Asabe, dake karkashin karamar hukmar Dala, na daya daga cikin unguwannin da mabiya Shi'a keda yawam jama'a, amma saboda kasancewa an baza jami'an unguwar, 'yan shi'ar basu samu damar yin wani wargi ba.

A Goron Duste, gidan tsohon shugaban mabiya kungiyar Shi'a, Muhammad Turi, babu kowa a waje, mabiya Shi'ar sun zauna a cikin gidajensu saboda jami'an tsaro da aka zube a yankin unguwar.

Wani mamaba a kungiyar IMN a Kano da ya yi magana da majiyar Legit.ng, ya ce, "mun fito da sanyin safiya, misalin karfe 6 na safe, kuma mun gaggauta yin al'amuran mu cikin kankanin lokaci don ganin ba a samu wata matsala ba.

"duk lokacin da aka kai wa mambobinmu hari, sai 'yan jarida su ce mun yi fada da jami'an tsaro. Ta yaya mutanen da basu da makamai zasu iya fada da ma'aikata. 'Yan jarida basa yi mana adalci a rahotanninsu."

Kazalika, kwamishinan 'yan sanda a jihar Kano, Ahme Iliyasu, ya sanar da jaridar 'The Nation'

cewa mabiya shi'ar basu gudanar da wani sha'ani domin tuna wa da ranar Ashoura ba a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel