Super Eagles ta tashi wasa canjaras da kasar Ukraine

Super Eagles ta tashi wasa canjaras da kasar Ukraine

Tawagar kwallon kafan Najeriya ta Super Eagles ta yi watsi da damar ta inda ta bari kasar Ukraine ta rama kwallayen da ta zura mata bayan ta shiga gaba da ci 2-0.

An dai tashi wasan ne canjaras da ci 2-2. Wannan wasan dai wasa ne na sada zumunta wanda aka buga a birnin Dnipro dake kasar Ukraine.

KU KARANTA:Gwamnatin Kaduna da kasar Denmark sun kulla yarjejeniyar bude katafaren kamfanin sarrafa madara

Dan wasan Najeriya Joe Aribo shi ne ya fara zura kwallo a raga bayan minti hudu kacal da take wasan, yayin dad an wasan gaban Super Eagles mai suna Victor Osimhen ya zura kwallo ta biyu a bugun daga kai sai mai tsaron gida a cikin mintuna 34 da soma wasan.

Sai dai kuma kash, murna ta komawa ‘yan wasan Super Eagles ciki saboda Oleksandr Zinchenko da Roman Yaremchuk sun farke kwallayen biyu kafin a hura tashin wasan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel