Kotun zaben shugaban kasa: Mun tabbatar da yin nasara - APC

Kotun zaben shugaban kasa: Mun tabbatar da yin nasara - APC

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ta nuna karfin gwiwar cewa ita ce za ta yi nasara a kotun zaben shigaban kasa, yayinda ake shirin yanke hukunci.

Babban sakataren APC na kasa, Mallam Lanre Issa-Onilu, ya bayar da tabbacin a wata hira da jaridar Daily Sun, inda ya kara da cewa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ta taimaka wa jam’iyya mai mulki wajen tabbatar shari’an a fiye da tunani.

“Bamu da wani dalili da zai sa muyi kokwanton samun nasara saboda PDP basu gabatar da wani kwakwaran abu da ya Saba doka akan mu ba. Ya zama dole mu gode na PDP kan taimaka mana da tayi wajen tabbatar da shari’anmu fiye da tunani.

“Muna fatan cewa tunda bamu baya lokacinmu ba sannan kuma basu da wani hujjar musanta ikirarinmu kamar lamarin takardar makarantar Shugaban kasar, wanda suka gaza kawo wani abu da zai nuna cewa ba mai inganci bane imma daga hukumar WAEC ko Cambridge; sun yi mana alfarma ne.

KU KARANTA KUMA: Uwargidar Fayemi ta tsallake rijiya da baya yayinda daliban FUOYE suka far ma ayarin motocinta

“Akan lamarin sakamakon, sun kawo duk abunda suka ga dama, sannan bamu san wanne suke sa ran kotun zabe ta dauka ba. Duk abun ya zama ba komai ba face kamanceceniya da yadda PDP ke gudana. Bamu shakkar cewa mune za muyi nasara,” inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel