Gwamnatin Kaduna da kasar Denmark sun kulla yarjejeniyar bude katafaren kamfanin sarrafa madara

Gwamnatin Kaduna da kasar Denmark sun kulla yarjejeniyar bude katafaren kamfanin sarrafa madara

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai a ranar Litinin 9 ga watan Satumba ya ce gwamnatinsa ta sanya hannu a kan wata yarjejeniya da kasar Denmark domin bunkasa sarrafa madarar shanu a jihar.

Gwamnan ya ce, an kirkiro da wannan sabon tsarin ne domin nunawa makiyaya cewa za su iya cin moriyar dabbobinsu ta hanyar amfani da zamani, ba tare da sun rika yin zirga-zirga ba daga wuri zuwa wuri.

KU KARANTA:Sojojin Najeriya na kama yara kanana da sunan Boko Haram – Kungiyar Human Right

El-Rufa’i ya sanya hannu a kan yarjejeniyar da wani kamfanin kasar Denmark. Sunan kamfanin Arla foods international wanda ya samu wakilcin mataimakin shugaban kamfanin, Steen Hadsdjerg.

Rahotanni daga jaridar Vanguard sun bayyana mana cewa, idan ana maganar ayyuka ne kamfanin zai samar da ayyukan yi sama da 50, 000 inda kuma ake sa ran za a kashe miliyan €100.

A cikin jawabin da Gwamna El-Rufai yayi ya bayyana dalilinsa na kulla wannan yarjejeniya, inda yake cewa, samar da sauki ga manoma da kuma mata wurin sarrafa madarar shanun shi ne burinsu.

Ta hanyar amfani da ire-iren wadannan kamfanoni, makiyaya za su fahimci albarkar da ke cikin kiwo da kuma hanyar cin amfaninsa cikin sauki.

“Akwai kamfanoni da yawa wadanda suka so mu kulla wannan alakar da su amma sai muka zabi Arla saboda shi ne kadai kamfanin da muke da yakinin cewa zai samar wa mutanenmu da abinda muke bukata a matsayinmu na gwamnati.” Inji El-Rufa’i.

Haka zalika, Jakadan Denmark a kasar Najeriya ya ce ofishinsa na jakadanci zai cigaba da bayar da gudunmuwa ga irin wadannan ayyuka domin cigaban Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel