Mabiya El-Zakzaky sun kai mana hari da gwafa amma ba su kashe su ba - 'Yan sanda

Mabiya El-Zakzaky sun kai mana hari da gwafa amma ba su kashe su ba - 'Yan sanda

Rundunar 'Yan sandan Najeriya ta zargi 'yan kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN) da jigar jami'anta da duwatsu, karafuna da gwafa yayin tattakin su na ranar Ashura a ranar Talata a Kaduna.

'Yan sanda da 'yan Shi'a mabiya Ibrahim El-Zakzaky sunyi arangama a garin Kaduna a yau Talata.

Kungiyar ta IMN ta yi ikirarin cewa 'yan sanda sun kashe mata mambobi uku tare da raunata wasu guda 10.

Amma a sanarwar da ya fitar, mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Kaduna Yakubu Sabo ya ce 'yan sanda sun tafi su tarwatsa 'haramtaciyyar taro' ne tare da warware cikinson motocci yayin da 'yan kungiyar suka kai musu hari kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Ya ce duk da gargadin da aka yi wa 'yan kungiyar kan tattakin, 'yan kungiyar na IMN sun fito kwansu da kwarkwata sun mamaye titin Nnamdi Azikwe da ke Kaduna da unguwar Kasuwan Mata da ke Zaria city inda suka tare titi tare da musgunawa masu ababen hawa.

Ya ce 'yan kungiyar ta IMN sun fito suna rera wakokin kiyaya ga gwamnati tare da neman sakin shugaban su da matarsa da ke tsare tun Disambar 2015.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Kotu ta kwace kujerar dan majalisar APC a jihar Kano

Sabo ya ce, "Yau misalin karfe 6.55 na safe an sanar da mu cewa mambobin haramtaciyar kungiyar IMN da aka fi sani da Shi'a sun fito sun mamaye babban titin Nnamdi Azikwe da ke Kaduna da kuma Kasuwan Mata da ke Zaria city don yin tattaki na ranar Ashura inda suka tare tituna tare da janyo cinkoson ababen hawa da musguwa masu ababen hawa."

"Kowa dai ya sani cewa gwamnatocin tarayya da na jihar Kaduna sun haramta ayyukan kungiyar a baya-bayan nan.

"Hakan yasa aka tura tawagar 'yan sanda cikin gaggawa domin tarwatsa haramtaccen taron da kuma warware cinkoson motoccin.

"Amma suna ganin 'yan sandan sai suka fara jifan su da duwatsu da karafuna ga gwafa. Lamarin ya yi tsamari kuma 'yan kungiyar suka tayar da rikici.

"Hakan yasa aka yi amfani da kankanin matsakaicin karfi don tawartsa su. Hukumar 'yan sanda tana son kowa ya sani cewa kawo yanzu ba ta samu rahoto a hukumance cewa wasu sun mutu ba kamar yadda 'yan kungiyar su kayi ikirari a yau."

Sabo ya shawarci al'umma su cigaba da gudanar da halastattun harkokinsu na yau da kulum kuma su sanar da hukumar idan sun ga wani abu da ba su amince da shi ba domin a dauki mataki cikin gaggawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel