Trump ya kori mai bashi shawara a kan harkokin tsaro, ya ce ra'ayinsu ya sha ban - ban

Trump ya kori mai bashi shawara a kan harkokin tsaro, ya ce ra'ayinsu ya sha ban - ban

A ranar talata ne shugana kasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa ya umarci mai bashi shawara a kan harkokin tsaro, John Bolton, da ya yi murabus saboda wasu dalilai banbancin ra'ayi da siyasa.

"Na sanar da John Bolton a daren jiya cewa aikinsa ya kare a 'White House' (fadar gwamnatin kasar Amurka). Bana iya amince da shawarwarin da yake bashi kan sha'anin da ya shafi tafiyar da gwamnati," kamar yadda Trump ya wallafa a shafnsa na Tuwita.

"Na bukaci ya ajiye aiki, kuma an bani takardarsa ta barin aiki da safiyar yau (Talata)," a cewar shugaban kasar, tare da bayyana cewa zai maye gurbinsa a cikin sati mai zuwa.

Sai dai, Bolton ya mayar wa Trump martani nan take a shafin Tuwita, inda ya ce "a daren jiya na sanar da shugaba Trump cewa zai yi murabus, amma sai yace zamu yi magana da safe".

Kazalika Bolton ya aika sako zuwa kafafen yada labarai a kasar Amurka a kan cewa ya yi murabus bisa radin kansa.

Faruwar lamarin ta bayar da mamaki a fadar 'white house' saboda bai wuce sa'a daya ba Trump ya sanar da cewa Bolton zai bayyana a wata tattauna wa tare da manema labarai tare da sakataren gwamnati, Mike Pompeo da ma'ajin sakatare, Steven Mnuchin.

Sa'a daya kafin sanarwar ta Trump, an ga Bolton na wallafa bayanai amadadin gwamatin Trump a shafinsa na Tuwita.

An dade ana ganin rashin dacewar mu'amalara aiki a tsakanin Trump da Bolton a matsayin shugaba da hadiminsa, saboda rashin amincewar ra'ayinsu a kan shiga sha'anin tsaron kasashen duniya.

A yayin da Trump ke son Amurka ta kebe kanta daga shiga batun tsaro a wasu kasashe, Bolton na da ra'ayin Amurka ta cigaba da zama a matsayin 'uwa da makabiya' a sha'anin tsaron duniya.

Source: Legit

Mailfire view pixel