Uwargidar Fayemi ta tsallake rijiya da baya yayinda daliban FUOYE suka far ma ayarin motocinta

Uwargidar Fayemi ta tsallake rijiya da baya yayinda daliban FUOYE suka far ma ayarin motocinta

Wasu daliban jami’ar tarayya da ke Oye, jihar Ekiti a ranar Talata, 10 ga watan Satumba, sun kai wa ayarin motocin matar gwamnan jihar Ekiti, Erelu Bisi Fayemi farmaki a hanyarta na dawowa daga rangaji a wasu kananan hukumomi.

Anyi zargin cewa daliban sun mamaye hanyar babban titin Oye-Ikole-Abuja domin hana ayarin motocin uwargidar gwamnan wucewa, tare da kudirin nuna fushinsu akan rashin samun wutar lantarki a garin.

An tattaro cewa daliban sun kara da jami’an tsaro da ke tare da uwargidar gwamnan, inda aka kawo cewa an kona biyu daga cikin jami’an tsaron sannan aka kwace bindigogi biyu.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa wasu mutane sun tsere da Misis Fayemi a cikin wata farar motar hilux domin tsiratar da rayuwarta.

An tsere da ita ne ta Ayegbaju Ekiti inda aka raunata jami’an gwamnati, yan jaridar da kuna jami’an yan sandan da ke tare da ita.

An rahoto cewa daliban sun tarwatse yan awanni bayan sun yi zanga-zangar rashin wutan.

Daga bisani zaman lafiya ya dawo sansanin daliban.

KU KARANTA KUMA: Kotun zabe ta fatattaki karar da yar takarar PDP ta shigar kan sanatan APC

Da yake martani, jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan Ekiti, Mista Caleb Ikechukwu, ya tabbatar da harin da aka kaiwa matar gwamnan.

Yayi bayanin cewa daliban sunyi zanga-zanga da safe sannan suka toshe hanyar babban titin Ifaki-Ikole-Omuo sannan suka hana ababen hawa wucewa ta dadin rai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel