Matasa sun yi zanga-zanga a kan yawan albashin 'yan majalisa, sun kona akwatin gawa

Matasa sun yi zanga-zanga a kan yawan albashin 'yan majalisa, sun kona akwatin gawa

Mutane sun sha mamaki a Legas a ranar Talata yayin da wasu matasa 'yan gwagwarmaya suka kona akwatin gawa domin yin zanga-zanga kan albashin da 'yan majalisar suke samu mai dan karen yawa.

Matasan karkashin jagorancin Shugaban Activists for Good Governance (AGG) Kwamared Declan Ihekaire sun ce ya dace 'yan majalisar da galibinsu 'yan jam'iyyar APC ne masu ikirarin canji su fara nuna misali ta hanyar rage albashi da allawus din su.

Sun ce albashi da allawus din 'yan majalisar ne ke yi wa arzikin kasar nan illa kuma ya zama dole a taka musu birki.

Mutane masu tafiya a kafa da wadanda ke cikin motoci sun taru suna kallon yadda matasan suka bankawa akwatin gawar mai dauke da rubutu neman a rage albashin 'yan majalisar wuta a kan titin Ipaja.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Kotu ta kwace kujerar dan majalisar APC a jihar Kano

A yayin da ya ke yi wa mahalarta taron jawabi, Ihekaire ya kallubalanci 'yan majalisar su rage albashi da allawus dinsu idan har da gaske suna son yi wa al'umma hidima ne.

Ya ce abin takaici ne yadda 'yan majalisar suka samu naira biliyan 4.6 a matsayin kudin 'wanke talauci' kuma suka saya motocci na biliyoyin naira yayin da ake ta faman kai ruwa rana kan batun albashi mafi karanci na N30,000.

A cewarsa, a matsayinsu na masu ikirarin kawo canji, ya kamata mambobin majalisa na 9 su nuna jagoranci na gari ta hanyar rage albashinsu da kuma yi wa kasa hidima.

"Ba wannan abin muke nema ba yayin da muka fattataki tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan daga kan mulki. Ya kamata 'yan majalisar su yi abinda ya dace," inji shi.

Shugaban ya ce tarihi ba zai manta da 'yan majalisar ba idan su kayi jarumtaka suka rage albashinsu domin cigaban kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel