Sojojin Najeriya na kama yara kanana da sunan Boko Haram – Kungiyar Human Right

Sojojin Najeriya na kama yara kanana da sunan Boko Haram – Kungiyar Human Right

Kungiyar nan mai fafutukar kare hakkin bil’adama ta Human Right Watch (HRW) ta ce rundunar sojin Najeriya na kama kananan yara da sunan ‘yan kungiyar Boko Haram.

A wani zance da kungiyar ta fitar a yau din nan Talata 10 ga watan Satumba, 2019, ta bayyana cewa akwai yara kanana da yawa wadanda rundunar sojin ke tsare da sub a tare da kai su kotu ba ko kuma barin su shakatawa.

KU KARANTA:Miliyoyin ‘yan Najeriya na cikin matsananciyar wahala ne a dalilin cin-hanci da rashawa – Buhari

Bugu da kari, kungiyar ta yi wani rubutu ne mai shafi 50 inda ta fadi abinda rundunar sojin ke yiwa yara kanana da sunan Boko Haram a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

“Ana matukar cin zarafin yaran nan ta hanyar barinsu da yunwa, duka ba dare ba rana, matsanancin zafi a dalilin sanyasu cikin matsatsen daki maras walwala.

“Akasarin wadanda muke magana a nan yara ne kanana. An tsare tsawon shekaru masu tarin yawa ba tare da wata ingantacciyar shaidar cewa lallai suna da hannu cikin ayyukan mayakan Boko Haram ba.” Inji Jo Becker.

Ya kara da cewa: “Da yawa daga cikin yaran ma wadanda suka tsira ne daga hare-haren Boko Haram. Sai ga shi kuma a maimakon a ce suna samun kulawa ta musamman hakan bai yiwu ba face akasinsa da suke kan gani.”

A karshe kungiyar ta HRW ta yi kira ga rundunar sojin Najeriya cewa ta yi amfani da tsarin Majalisar dinkin duniya domin a yiwa yaran abinda ya fi dacewa da su.

Sai dai kuma a bangare guda, kakakin Hedikwatar tsaron sojin Najeriya, Kanal Onyeama Nwachukwu ya karyata wannan maganr inda ya ce wannan abu cin fuska ne ga jami’an soji gaba daya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel