Mun gurgunta kungiyar Boko Haram, za mu karasa murkushe birbishinsu - Buhari

Mun gurgunta kungiyar Boko Haram, za mu karasa murkushe birbishinsu - Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce 'yan kungiyar Boko Haram da su kayi saura a yankin Arewa maso Gabashin kasar nan 'yan bindiga ne, "kuma za mu cigaba da daukan su a hakan."

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi bakuncin Shugaban Kungiyar ICRC a fadar gwamnati da ke Abuja a ranar Talata.

Buhari ya jadada cewa an ruguza kungiyar Boko Haram amma har yanzu akwai wasu mambobin kungiyar da su kayi saura da ke adabar mutane a Tafkin Chadi da kewaye.

"Haka ne yasa muke hadin gwiwa da Chadi, Kamaru, Jamhuriyar Nijar da sauran kasashe. Muna kuma amfani da sojojin saman mu kamar yadda ya kamata. 'Yan ta'adda ne kuma za mu cigaba da daukan su a hakan," a cewar shugaban kasar.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Kotu ta kwace kujerar dan majalisar APC a jihar Kano

Shugaban kasar ya ce gwamnati ta mayar da hankali kan gyara kayayyakin gwamnati da suka lalace tare da tallafawa 'yan gudun hijira da mutanen da suka rasa muhallansu saboda su koma gidajensu.

Ya yabawa taimakon da ICRC da wasu kungiyoyi masu taimakon mutane inda ya jadada cewa gwamnati ba za tayi kasa a gwiwa ba wajen ganin an bawa dukkan mutanen tallafin da suke bukata.

"Halin da 'yan gudun hijira suke ciki abin tausayi ne. Wasu yaran ba su san inda iyayensu suke ba ko daga inda suka fito.

"Muna mayar da hankali kan basu ilimi da kulawa da lafiyarsu tare da sake gina garuruwa da aka lalata.

"A baya kungiyar tana karkashin jagorancin Janar Theophilus Danjuma ne amma yanzu Manjo Janar Tarfa ke jagorancin ta. Muna ware kudade masu yawa don wadannan ayyukan," a cewar shugaban kasar.

Ya kuma ce ana samun nasara wurin fahimtar da al'umma cewa ta'addanci ba shi da alaka da addini.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel