Kotun zabe ta fatattaki karar da yar takarar PDP ta shigar kan sanatan APC

Kotun zabe ta fatattaki karar da yar takarar PDP ta shigar kan sanatan APC

Kotun sauraron kararrakin zaben majalisar dokokin tarayya a jihar Oyo ta soke wani kara da ke kalubalantar nasarar Fatai Buhari na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben sanatan Oyo ta arewa.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito cewa Mulikat Akande ta jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta kalubalanci kaddamar da Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben sanatan Oyo ta arewa a ranar 23 ga watan Fabrairu.

Sauran wadanda ake kara a lamarin sune hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da APC.

Kotun zaben, wacce Justis Anthony Akpovi ke jagoranta tare da Justis Sambo Daka da Justis Chinyere Ani a matsayin mambobi, ta soke karar.

Daka, wanda ya karanto hukuncin, yace mai karar ya kira shaidu tara da kayayyaki 96.

Ya bayyana cewa mafi akasarin takardun da ta gabatar basu da nasaba da karar sannan kuma cewa sun kasance takardu marasa amfani.

KU KARANTA KUMA: Sanatan Plateau: Jam’iyyar PDP tayi gagarumar nasara a kotun zabe

Daka ya kuma bayyana cewa mai karar ya gaza tabbatar da zarginta na zarcewar kuri’u da rashin bin dokar zabe da zai sa kotun tayi umurnin sake sabon zabe.

Kotun zaben tayi watsi da karar sannan ta ci tarar mai karar N150,000.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel