Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta kama 'yan damfara 167 cikin kwanaki 21

Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta kama 'yan damfara 167 cikin kwanaki 21

- Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta ce ta kama 'yan damfara 167 cikin makonni 3

- Hakan ya faru ne sakamakon aikin hadin guiwar da tayi da FBI

- Hukumar ta yi kira ga matasa da su dage da neman na kansu a maimakon fadawa abinda zai kaisu ga dana sani

Hukumar yaki da rashawa ta EFCC a ranar Talata ta ce hadin guiwarta da hukumar bincike ta Amurka(FBI) ta jagoranci kama 'yan Najeriya 167 da take zargi da damfara.

Mukaddashin Shugaban hukumar, Ibrahim Magu, ya sanar da hakan ta bakin wakilinsa, Mohammed Abba.

Magu yace aikin da suka yi da FBI din yasa sun kwato har dala 169,850 tare da kuma Naira miliyan 92 daga hannun 'yan damfarar.

Ya kara da cewa, an samo motocin alfarma 4 da kuma filaye a Legas da Abuja yayin binciken.

KU KARANTA: Sowore: Anyi musayar yawu tsakanin lauya da mai shari'a

"Binciken da hukumar yaki da rashawa tayi da hadin guiwar FBI wanda ya dau sati uku anyi shi ne don bankado 'yan damfara na yanar gizo."

"Kafin nan, hukumar tayi kokari wajen bankado 'yan damfarar ta hanyar kai samame maboyarsu, gurfanar dasu da kuma dauresu."

"Aikinmu tare da FBI ya kawo cigaba mai yawa ta hanyar kama 'yan damfarar da kwace dukiyoyi ko kudaden da suka damfara. Wadanda ake zargin kuma aka kama za a gurfanar dasu tare da yanke musu hukuncin da ya dace," inji shi.

A don haka ne, Magu ke horar kafafen yada labarai da su cigaba da wayarwa tare da ilimantar da masu ruwa da tsaki akan bukatar goyon bayan cigaba da yaki da almundahanar kudade.

Yace hakkin al'umma ne wayar da kan matasa akan bukatar gujewa laifi.

"Inaso in sanar da cewa babu wata hanya mai sauki ta cin nasara da ta wuce aiki tukuru. A don haka ne muke kiran matasa da su daina rudar kansu gudun karewa a danasani."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel