Zaben 2019 :Dino Melaye ya daukaka karar hukuncin da kotun zabe ta yanke masa

Zaben 2019 :Dino Melaye ya daukaka karar hukuncin da kotun zabe ta yanke masa

Sanata Dino Melaye ya daukaka karar hukunci da kotun zaben Jihar Kogi ta yanke a kan zabensa inda ta soke nasarar tasa gaba daya. Jaridar Punch ta ruwaito cewa Melaye ya daukaka karar wannan hukunci na ranar 23 ga watan Agusta.

Rahotanni daga jaridar Premium Times sun kawo mana sakamakon abinda ya faru har aka tsige Dino Melaye (PDP, Kogi ta Yamma) a kotun zaben Jihar Kogi.

KU KARANTA:Wani matashi ya sace babur din danuwansa kuma ya aika shi lahira

Da yake zartar da yanke hukuncin Jastis A.O. Chijioke wanda shi ne alkalin dake sauraron karar ya ce akwai magudi mai tarin yawa a cikin zaben.

Majiyar kamfanin dillancin labaran Najeriya wato NAN ta ruwaito cewa Melaye ne ya lashe zaben inda ya samu kuri’a 85,395 a yayin da abokin takararsa na APC Smart Adeyemi ya samu kuri’a 66,902.

Sai dai kuma Adeyemi da jam’iyyarsa ta APC sun ki amincewa da sakamakon zaben inda suke cewa akwai lauje cikin nadi a dangane da zaben.

A cewar Adeyemi a tafka magudi mai tarin yawa, ta hanyar sabawa dokokin dake a cikin kundin tsarin zabe na shekarar 2010 (wanda aka yiwa garambawul).

Kotun zaben ta ce babu abinda zai warware wannan matsalar idan ba sabon zabe a ka sake yi ba, inda kuma ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta da ta yi gaggawar shirya wani sabon zabe nan da kwana casa’in.

Dino Melaye zai cigaba da kasancewa a matsayinsa na sanata har zuwa lokacin da Kotun daukaka kara dake Abuja za ta yanke na ta hukuncin game da wannan shari’a.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel