Tsantseni: Buhari ya tara kudin shiga naira tiriliyan 2 a wata 6 kacal

Tsantseni: Buhari ya tara kudin shiga naira tiriliyan 2 a wata 6 kacal

Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta tara kudaden shiga da suka kai naira tiriliyan 2 a cikin watanni 6 kacal, daga watan Janairu zuwa watan Yuni na shekarar 2019, inji rahoton kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito daraktan ofishin kasafin kudi a fadar shugaban kasa, Ben Akabueze ne ya bayyana haka yayin da yake gabatar da jawabi game da tsare tsaren kashe kudi na gwamnatin tarayya na matsakaici zango a Abuja.

KU KARANTA: Tattakin Ashura: Yan Shia sun sake yin artabu da Yansandan Najeriya a Bauchi

A jawabinsa, Akabueze yace gwamnatin tarayya ta kashe kimanin kudi naira tiriliyan 3.3, sa’annan ana fitar da kimanin gangar danyen mai daya kai miliyan 1.6 a kowanne rana daga Najeriya.

Mista Akabueze yace gwamnati ta samu kudaden shiga daya kai naira tiriliyan 4 a shekarar 2018, tare da kashe kimanin naira tiriliyan 7.4, sa’annan ta kashe naira tiriliyan 1.7 wajen samar da manyan ayyuka.

Sai dai jami’in kasafin kudin yace akwai yiwuwar samun cigaba a kudaden shiga da gwamnatin Najeriya ke samu, musamman duba da cewa kamfanin man fetir ta Najeriya ta bayyana cewa za’a samu karin adadin gangar danyen mai da ake fitarwa a Najeriya zuwa ganga miliyan 2.1.

A wani labarin kuma, duk wani ma’aikacin gwamnatin tarayya dake karkashin wata ma’aikata ko hukumar gwamnati da baya cikin tsarin biyan albashi na bai daya watau, IPPIS-Integrated Payroll and Personnel Information System ba zai sake samun albashinsa ba, inji ministar kudi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel