An gudu ba a tsira ba: Daga zuwa kai wa barayi kudin fansa shima anyi garkuwa da shi

An gudu ba a tsira ba: Daga zuwa kai wa barayi kudin fansa shima anyi garkuwa da shi

- Wani mutumi da yaje domin kai wa barayi kudin fansar da suka bukata shima sunyi garkuwa da shi

- Mutumin dai yaje domin ya bayar da kudin fansar mahaifiyar tsohon shugaban kwallon kafa na Najeriya Samson Siasia

- Yanzu dai kwanaki hamsin kenan da sace mahaifiyar shugaban kungiyar kwallon kafar inda suka bukaci a basu naira miliyan hamsin

Florance Donana, daya daga cikin mutanen da aka sace tare da mahaifiyar tsohon shugaban kwallon kafa Siasia, Beauty Ogere, ta samu ta sha dakyar daga hannun barayin da suka sace su din.

Barayin da suka sace Ogere a lokacin tana gidan danta dake Odoni cikin karamar hukumar Sagbama a jihar Bayelsa da misalin karfe 2 na dare, sun kuma sace Donana mai shekaru 66 da jikarta mai shekaru 17 a duniya.

Sai dai kuma bayan 'yan uwan Donana sun yarjejeniya akan kudin da za'a kai domin a sako su, wanda ya tafi domin ya kai kudin shima masu garkuwa da mutanen sun kama shi bayan sun karbi kudin, sai dai kuma sun saki Donana ne kawai.

KU KARANTA: Allah wadan naka ya lalace: An kama Malamin Addini da yake sanya mabiyansa mata suyi tsirara ya dinga daukar su hoto

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, wani mutumi da ya caccaki kwamishinan 'yan sandan jihar ta Bayelsa, Uche Anozia akan cewa baya tabuka komai wajen ganin an dawo da iyayen tsohon mai tsaron raga da kuma mahaifiyar tsohon shugaban kwallon kafa na Super Eagle wanda suke hannun 'yan bindigar na tsawon kwanaki 50.

Barayi wadanda suka kira Siasia a waya kwanaki biyu bayan sun sace su, sun bukaci a basu naira miliyan saba'in. Daga baya kuma suka rage kudin ya dawo miliyan hamsin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel