Allah wadan naka ya lalace: An kama Malamin Addini da yake sanya mabiyansa mata suyi tsirara ya dinga daukar su hoto

Allah wadan naka ya lalace: An kama Malamin Addini da yake sanya mabiyansa mata suyi tsirara ya dinga daukar su hoto

- Rundunar 'yan sandan jihar Oyo sun cafke wani mutumi da ya nuna shi malamin addini ne ashe na karya ne

- Mutumin yana daukar hotunan mata mabiya cocinshi tsirara idan ya gama zina da su

- Bayan haka mutumin yana yiwa matan barazanar zai wallafa hotunan su a kafar sadarwa idan har suka ce zasu bar cocin shi ko kuma su daina kwanciya da shi

Rundunar hukumar 'yan sanda ts jihar Oyo ta kama wani malamin addini mai shekaru 62 a duniya mai suna Olusegun Oyetunji, da laifin daukar mata mabiya cocinsa hotuna tsirara.

Lamarin ya samo asali ne a lokacin da wata mata mai shekaru 28 da ya dauki hotunanta ta gano cewa Faston karya ne. Hakan yasa Oyetunji yayi mata barazanar zai wallafa hotunanta da ya dauka a shafukan sada zumunta na zamani, idan har ba ta dawo cocin shi ba, ko kuma ta ce za ta daina kwanciya da shi.

Domin tabbatar da cewa ta goge hotunanta a wayar shi, sai tayi masa wayo ta ce masa zata dawo, har ta samu ta karbi wayarshi, abin mamaki kawai sai ganin hotunan wasu matan tayi da yawa a cikin wayar shi, ciki hadda wata budurwa mai shekaru 17.

KU KARANTA: Tirkashi: Wasu 'yan majalisu sun bawa hammata iska a cikin coci akan kujerar mulki

Faston ya hadu da wannan karamar yarinya ne a lokacin da ta dauke shi wajen mahaifiyar ta domin yayi mata addu'a. Ya gayawa budurwar cewa tana da matsalar da addu'ar shi ce kawai za ta zama mafita ga daginta.

Hakan yasa ya nemi ta same shi a coci domin yi mata addu'a ta musamman, a lokacin addu'ar ne ya dauki hotonta tsirara inda yace mata zai yi amfani da shi yayi mata addu'a.

A sanadiyyar hakane Oyetunji har ya fara yin zina da wannan matashiyar budurwa mai shekaru 17.

Da aka bincike shi, Oyetunji ya bayyana yadda ya fara lalata da mace ta farko a cikin mabiyansa, wato matar nan mai shekara 28.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel