Tirkashi: Wasu 'yan majalisu sun bawa hammata iska a cikin coci akan kujerar mulki

Tirkashi: Wasu 'yan majalisu sun bawa hammata iska a cikin coci akan kujerar mulki

- An samu sabani tsakanin 'yan majalisun mazabar Kiharu dake kasar Kenya

- Lamarin ya samo asali ne yayin da rikici ya balle akan wanda yake da iko a mazabar ta Kiharu, inda kowa yake nuna yana da iko da mazabar

- Lamarin ya faru a wajen wani taro da aka gabatar a wata coci dake yankin Muranga cikin kasar ta Kenya

'Yan siyasa biyu na kasar Kenya da wasu 'yan majalisu guda biyu, Ndindi Nyoro da Maina Kamanda sun bawa hammata iska jiya a Gatui Catholic Church dake Muranga, akan wanda zai mulki yankin Kiharu.

Rikicin ya samo asali ne dai bayan Nyoro ya shigo cocin wacce Kamanda shima ya halarta shi da wasu 'yan majalisu na Kieleweke. Nyoro ya dakatar da taron, inda ya bayyana cewa shi kadai ne yake da ikon da zai gayyaci wadanda za su wannan taro na coci a yankin Kiharu.

"Ni ne dan majalisa kuma ni kadai ne nake da ikon gayyatar mutanen da nake so suyi aiki a mazabar nan. Ina girmama Maina Kamanda a matsayinsa na Uba kuma babba a wannan matsaba ta mu, amma bazan iya bari ya dauko kafa tun daga Nairobi ba ya zo don ya jagoranci taron mu," in ji Nyoro.

KU KARANTA: Tirkashi: Na daina zuwa coci ne bayan na gano addinin Kiristanci buge-bugen iska ne - Efia Odo

Sannan ya kara da cewa babu yadda za ayi a cigaba da gabatar da wannan taron tunda har ba a gayyace shi ba, kuma taro ne da ake yi a mazabar shi.

Wani bidiyo da yake ta yawo ya nuna lokacin da 'yan majalisun guda biyu suke nunawa juna yatsa a wajen taron wanda 'yan majalisu kimanin 20 suka halarta, kafin daga baya suka kama wuyar rigar juna za su bawa hammata iska.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel