Sanatan Plateau: Jam’iyyar PDP tayi gagarumar nasara a kotun zabe

Sanatan Plateau: Jam’iyyar PDP tayi gagarumar nasara a kotun zabe

Kotun sauraron kararrakin zaben majalisar dokokin tarayya da ke zama a Jos, jihar Plateau, ta yi watsi da karar da Sanusi Inuwa na jam’iyyar United Progressives Party (UPP), ya shigar akan Sanata Istifanus Gyang na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), akan rashin inganci.

Kotun zaben karkashin jagorancin Justis Theophilus Nzeogwu ta yanke cewa ba za a iya ci gaba da sauraron karar ba don haka ta soke shi kan hujjar cewa mai karar ya gaza tabbatar da shari’arsa.

“Mai karar ya gaza tabatar da kararsa saboda bai gabatar da kowani takarda da ke nuna cewa an zabe shi domin yin takarar kujerar sanatan Plateau ta arewa ba,” inji Nzeogwu.

Da yake jawabi jim kadan bayan yanke hukuncin, hadimin sanatan a kafofin watsa labarai, Musa Ashoms ya bayyana hukuncin a matsayin “nasara ga zabin mutane.”

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago za su gana a ranar 16 ga watan Satumba kan karancin albashi

A wani labarin kuma mun ji cewa jam’iyyar APC ta reshen jihar Abia, ta yi watsi da hukuncin da kotu ya yanke game da zaben kujerun ‘yan majalisa inda Sanatan ta mai wakiltar Abia ta Arewa ya rasa kujerarsa.

Sakataren yada labarai na jam’iyyar APC a Abia, Kwamred Benedict Godson, ya nuna cewa APC ba za ta amince da sakamakon wannan shari’a ba. Benedict Godson ya nuna cewa za su koma kotu.

Da Benedict Godson yake magana da Manema labarai a Ranar Litinin bayan kotu ta karbe kujerar Sanata Orji Uzor Kalu, ya bayyana cewa za su bi duk wata hanya domin daukaka kara a kotu.

Haka zalika Jagoran na APC a Abia, ya yi kira ga Magoya bayan tsohon gwamna Orji Uzor Kalu, su kwantar da hankalinsu. Godson ya yi wannan kira ne a Garin Umuahia a madadin jam’iyyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel