Kashin farko na 'yan Najeriya mazauna kasar Afirka ta Kudu zasu dawo gida gobe

Kashin farko na 'yan Najeriya mazauna kasar Afirka ta Kudu zasu dawo gida gobe

- Kashin farko na 'yan Najeriya mazauna kasar Afirka ta kudu za su dawo gida Najeriya gobe

- Jirgin zai tashi ne daga birnin Johannesburg da karfe 9 na safe

- Ministan harkokin waje kuma, Mr Onyeama ya ce gwamnati za ta dau nauyi jigilar 'yan Najeriyar

Babban wakilin Najeriya a Johannesburg, Godwin Adama, ya ce kashi na farko na 'yan kasar Najeriya da za su dawo daga kasar Afirka ta Kudu zasu iso Legas a ranar Laraba.

Adama ya sanar da kamfanin dillancin labarai hakan ne a tattaunawar waya da yayi da su.

Kashi na farkon za su bar kasar Afirka ta Kudun ne a ranar Laraba da karfe 9 na safe.

Babban wakilin ya sanar da cewa kamfanin jiragen sama na Air Peace ya nu na bukatar kwaso 'yan Najeriya 600 da ke da burin dawowa gida.

"Jirgin farko zai ta so ne da karfe 9 na safe a ranar Laraba dauke da fasinjoji 320. Jirgi na biyu kuma zai ta so ne a ranar Alhamis."

"Muna da sama da mutane 600 da su ka nuna bukatar dawowa gida."

A ranar Litinin da ta gabata ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci da a kwaso 'yan Najeriya mazauna kasar Afirka ta kudu masu bukatar dawowa gida sakamakon harin da 'yan kasar ke kaiwa 'yan kasashen da ba nasu ba.

Buhari ya bada umarnin ne bayan rahoton da ya samu daga wakilai na musamman da ya tura kasar Afirka ta kudun.

Kamfanin dillancin labarai ya ruwaito cewa Shugaban kamfanin Air Peace, Allen Onyeama, a satin da ya gabat ya dau nauyin dawo da 'yan Najeriya mazauna kasar a kyauta.

"Kamfanin Air peace a shirye ya ke da goyon bayan gwamnatin Najeriya ta hanyar bada jirgin sama mai lamba B777 don kwaso 'yan kasar zuwa gida," inji Onyeama.

Kamfanin ya shawarci masu dawowar da kada su biya kudin tikitin jirgi daga kasar Afirka ta Kudun zuwa Legas. Idan kuma sun biya, su koma don karbar kudinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel