Abia: Ba za mu amince da shari’ar Sanata Orji Kalu ba – Inji Jam’iyyar APC

Abia: Ba za mu amince da shari’ar Sanata Orji Kalu ba – Inji Jam’iyyar APC

Mun ji cewa jam’iyyar APC ta reshen jihar Abia, ta yi watsi da hukuncin da kotu ya yanke game da zaben kujerun ‘yan majalisa inda Sanatan ta mai wakiltar Abia ta Arewa ya rasa kujerarsa.

Sakataren yada labarai na jam’iyyar APC a Abia, Kwamred Benedict Godson, ya nuna cewa APC ba za ta amince da sakamakon wannan shari’a ba. Benedict Godson ya nuna cewa za su koma kotu.

Da Benedict Godson yake magana da Manema labarai a Ranar Litinin bayan kotu ta karbe kujerar Sanata Orji Uzor Kalu, ya bayyana cewa za su bi duk wata hanya domin daukaka kara a kotu.

Haka zalika Jagoran na APC a Abia, ya yi kira ga Magoya bayan tsohon gwamna Orji Uzor Kalu, su kwantar da hankalinsu. Godson ya yi wannan kira ne a Garin Umuahia a madadin jam’iyyar.

“Mun yi watsi da hukuncin da kotun da ke sauraron karar zabe ta yi gaba daya. Mu na kira ga kowa; Mutanen Abia, Magoya bayan jam’iyyar APC da Mabiyanmu su kwantar da hankalinsu.”

KU KARANTA: APC ta doke PDP a gaban kotu a karar kujerar Sanatan Legas

Sakataren yada labaran na APC ya kara da cewa: “Za mu bi duk wata hanya ta shari’a wajen ganin mun daukaka wannan kara a kotu.” Hakan na nufin APC za ta tafi gaban kotun daukaka kara.

Kotun da ke sauraron korafin zaben da aka yi a jihar Abia ta rusa nasarar da .Orji Uzor Kalu ya samu a matsayin Sanata mai wakiltar Abia ta Arewa kamar yadda Mao Ohuabunwa ya nema.

Sanata Ohuabunwa na jam’iyyar ya kalubalanci nasarar da tsohon gwamnan na Abia ya samu a karkashin APC. Alkalai kuma sun gamsu cewa ba Uzor Kalu bane halataccen Sanatan yankin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel