Tattaunawar sulhu: Gwamnatin Katsina ta saki yan bindiga 6 dake hannunta

Tattaunawar sulhu: Gwamnatin Katsina ta saki yan bindiga 6 dake hannunta

Gwamnan jahar Katsina, Aminu Bello Masari ya sanar da sakin wasu gagga gaggan yan bindiga guda 6 dake kame a hannun gwamnati a sakamakon tattaunawar sulhu da gwamnatin Katsina ta fara yi da yan bindigan, inji rahoton Punch.

Masari ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da manema labaru jim kadan kafin a kammala tsare tsaren sakin yan bindigan, sai dai gwamnan bai bayyana sunayen yan bindigan ba, saboda tsaro.

KU KARANTA: Ina neman Bilkisu ta bani y’ay’ana 3 tun da ta sake aure – Hassan ya roki kotu

A madadin yan bindiga 6 da gwamnan ya saki, ya bayyana cewa yan bindiga zasu sako mutane 20 daga cikin mutanen dake hannunsu a ranar Talata, 10 ga watan Satumba, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

Ko a daren Litinin, sai da wasu tubabbun yan bindiga guda hudu a kauyen Shinfida dake cikin karamar hukumar Jibia suka mika ma Gwamna Masari bindigunsu guda biyu kirar AK 47 tare da alburusai da dama.

Tubabbun yan bindigan sun hada da: Abdullahi Mairafi, Audu Danda, Ardo Nashawali da Sale Dangote, haka zalika yan bindigan sun yi alkawarin ba zasu sake komawa ga miyagun halayyarsu ba, kuma zasu yi aiki tukuru wajen tabbatar da zaman lafiya a Katsina.

Sai dai Abdullahi Mairafi ya nemi gwamnatin jahar Katsina ta samar da ababen more rayuwa ga jama’an karkara musamman Fulani makiyaya, kamar su asibitoci, madatsan ruwa da makarantu domin samun saukin rayuwa.0

Tun da fari, yan bindigan sun saki akalla mutane biyar ciki harda mata uku wadanda yan fashin suka yi garkuwa da su a sanadiyyar yarjejeniya zaman lafiya da aka kulla tsakanin gwamnatin jihar da yan bindigan.

Masari ne ya bayyana haka a yayinda yake hira da wasu tubabbun yan fashi a kauyen Baranda a karamar hukumar Batsari da ke jihar, inda yace an saki mutanen kuma an mikas su ga iyalansu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel