Kotu ta bada izinin a kamo wani dan Majalisar Jihar Bauchi

Kotu ta bada izinin a kamo wani dan Majalisar Jihar Bauchi

Wata kotu a jihar Bauchi ta bada izinin a kamo mata dan majalisar dokokin Jihar Bauchi mai wakiltar gundumar Zaki a bisa bijirewa sammacin da kotun ta aika masa. Sunan wannan dan majalisar Muktar A. Sulaiman.

Jastis Ahmed Shuaibu wanda shi ne alkalin kotun ya bada izinin a kamo masa dan majalisar ne a dalilin rashin mutunta sammacin da kotun ta aika masa inda ya ki zuwa kotun.

KU KARANTA:An daga jana’izar Mugabe har illa masha Allahu

Mu’azu Ahmed ne ya shigar da dan majalisar kara a cikin wata takarda mai lamba CMCBH/854/19 a ranar 15 ga watan Agusta, 2019 inda yake zargin dan majalisar da aikata wasu miyagun laifukan da suka ci karo da sashe na (143) (D) na kundin kotun miyagun laifuka.

Mai karar ya ce shi dai wannan dan majalisar yayi amfani ne da shekaru na karya kunshe a cikin takardun fom CF001 da ya kaiwa hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC domin tsayawa takarar gundumar Zaki ta 1 a majalisar dokokin Bauchi.

Ahmed ya kara da cewa: “Ya shirya wata babbar karya a gaban kotun Majistare inda ya sake tabbatar da wannan shekarun nasa na karya kamar yadda suke a cikin fom CF001 wanda ya bai wa INEC.”

Bugu da kari, Ahmed ya kara fadin cewa tun daga lokacin da ya shigar da wannan karar kotu yake fuskantar baraza daga bangaren wannan dan majalisar da yake kararsa.

A dalilin hakan ya roki kotu da ta shiga tsakaninsa da dan majalisar ta hanyar gurfanar da shi saboda laifukan da ya aikata wadanda suka sabawa kundin kotun muggan laifuka.

https://www.dailytrust.com.ng/court-issues-arrest-warrant-on-bauchi-house-of-assembly-member.html

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel