Yemi Osinbajo zai kafa rugar dabbobi a Jihar Adamawa a Yau

Yemi Osinbajo zai kafa rugar dabbobi a Jihar Adamawa a Yau

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, zai kai ziyara jihar Adamawa a Ranar Talata, 10 ga Watan Satumba, 2019, domin kaddamar da shirin gwamnatin tarayya na habaka rugar dabbobi.

Kamar yadda mu ka ji labari dazu, Farfesa Yemi Osinbajo zai ziyarci jihar ne domin bude wannan shirin kiwo na National Livestock Transformation Plan, NLTP wanda wasu ke kira RUGA.

Ana sa rai wannan tsari zai yi aiki daga 2019 zuwa 2028 a kokarin da gwamnatin Najeriya ke yi na kawo karshen rikicin Makiyaya da Manoma. An dade ana fama da wannan matsala a kasar.

Gwamnatin tarayya da sa hannun gwamnonin jihohi a karkashin majalisar NEC mai kula da tattalin arzikin kasar ta amince da wannan shiri da Mataimakin shugaban kasa ne ke jagoranta.

Gwamnatin Najeriya za ta soma dabbaka wannan shiri ne a wasu jihohi bakwai wadanda su ka hada da; Adamawa, Benuwai, Kaduna, Filato. Sauran jihohin su ne Nasarawa, Taraba da Zamfara.

KU KARANTA: An fara kuka bayan Gwamnatin Buhari ta garkame iyakoki

Osinbajo zai kaddamar da wannan tsari na NLTP ne domin tabbatar da wannan shiri da gwamnoni da sauran manya su ka amince da shi. Osinbajo ya ce wannan tsari ya sha banban da RUGA.

Manema labarai sun rahoto cewa za a bude wannan shiri ne a karon farko a Yola. Wannan sabon tsari zai gyara harkar kiwo tare da kawo hanyoyin zamani na samun nama da kuma nonon dabbobi.

Bugu da kari, a dalilin wannan tsari na noma, za a kawo karshen rikicin da aka saba samu tsakanin Manoma da Makiyaya. Shirin na NLTP za kuma bunkasa tattalin arzikin Najeriya ta aikin gona.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel