Bayanin BPP kan kwangiloli ya na iya batar da Jama’a - Fashola

Bayanin BPP kan kwangiloli ya na iya batar da Jama’a - Fashola

Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, ya bayyana cewa wasu bayanai da ake alakantawa ga hukumar BPP a Najeriya game da yadda ake kara kudin ayyuka a Najeriya na iya batarwa.

Hukumar BPP ta fito ta ce ta adana Naira biliyan 26 a shekarar 2018 kurum bayan ta sake duba wasu kwangilolin da jami’an Najeriya su ka bada a ma’aikatu da hukumomi da sassan gwamnati.

Raji Tunde Fashola ya nemi BPP ta fito ta yi wa Duniya bayani da kyau game da maganar da ta yi na cewa an rage mafi yawon kason wannan kudi ne daga wani aiki da aka bada a ma’aikatarsa.

A wani jawabi da Mai girma Ministan kasar ya yi ta bakin Hadiminsa, Hakeem Bello, ya fito ya ce:

“Hankalin Ministan ayyuka da gidaje ya zo ga wasu kanun labarai da ke yawo wanda aka alakanta su ga hukumar BPP a kan yadda ta adana Biliyan 26 a 2018 ta hanyar rage kudin da aka lafta a wasu kwangiloli, wanda wasu su ka fito daga ma’aikatar wuta da ayyuka da gidaje”

KU KARANTA: Dalilin da ya sa mu ka sha kashi a hannun PDP a Ribas – Shugaban APC

Ministan ya cigaba da cewa:

“A matsayinmu na ma’aikatu a gwamnati guda, bai dace a maida martani ba. Amma yanayin yadda ake karkatar da wannan rahoto a kafafen labara ya jawo dole mu fito mu yi wa jama’a karin haske.”

“Duk wanda ya karanta dokokin BPP ya san cewa babu wasu kwangiloli da aka karawa kudi domin ba a bada kwangila har sai hukumar BPP ta amince tn farko. Don haka babu wani coge da aka yi.”

A wannan dogon jawabi da Ministan ya yi, ya musanya cewa ya aikata ba daidai ba wajen raba kwangiloli a baya. Babatunde Fashola ya ce ya zauna da Masana wejen duba dokokin BPP kafin ya yi aiki.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel