An daga jana’izar Mugabe har illa masha Allahu

An daga jana’izar Mugabe har illa masha Allahu

An daga jana’izar tsohon Shugaban Zimbabwe, Robert Mugabe wadda da aka sanya za ayi a ranar Lahadi har sai yadda hali ya yiwu.

Iyalan marigayin ne suka sanarwa jaridar Zimlive da wannan labarin. A cewar wani da uwan marigayin Leo Mugabe ya ce ya zama wajibi a yiwa marigayin jana’iza irin ta gargajiya.

KU KARANTA:Ina neman Bilkisu ta bani y’ay’ana 3 tun da ta sake aure – Hassan ya roki kotu

Leo ya ce: “Mugabe babban mutum ne, a dalilin hakan ya zama dole mu yi masa jana’izar gargajiya. Har yanzu sarakunanmu ba su fada mana yadda jana’izar za ta kasance ba da kuma wurin da za a bizne shi.”

Idan baku manta ba dai, Robert Mugabe ya rasu ne ya na da shekaru 95 ranar Juma’a 6 ga watan Satumba a kasar Singapore inda ya je domin a duba lafiyarsa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel