Masu garkuwa da mutane sun sako mahaifiyar babban dan siyasa a Jigawa bayan matsin lamba

Masu garkuwa da mutane sun sako mahaifiyar babban dan siyasa a Jigawa bayan matsin lamba

Masu garkuwa da mutane sun sako Hajiya Ladi, mahaifiyar Yahaya Muhammad, tsohon mamba a majalisar dokokin jihar Jigawa.

An sako dattijuwar ne bayan ta shafe kwanaki shidda a hannun masu garkuwa da mutane, an sace ta a ranar 2 ga watan Satumba a kauyen Danladin Gumel dake yankin karamar karamar hukumar Maigatari.

Sai dai, an samu mabanbantan rahotanni dangane da yadda ta samu kubuta daga hannun 'yan ta'addar da suka sace ta.

Wani dan cikin gida, mai alaka da dattijuwar, ya shaida wa gidan Talabijin cewa an sako Hajiya Ladi ne bayan an biya miliyan N12 a matsayin kudin fansa.

Amma rundunar 'yan sanda ta musanta hakan tare da bayyana cewa bata da masaniyar cewa an biya kudin fansa kafin 'yan bindigar su sako ta.

"Jiya (Litinin) aka sako ta bayan 'yan bindigar sun sha matsin lamba daga rundunar 'yan sanda. Basu da wani zabi da ya wuce su sake ta.

"Ba mu da wata masaniya a kan biyan kudin fansa," a cewar kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Jigawa, DSP Abdul Jinjiri.

DUBA WANNAN: Rubdugu: Sojoji, 'Civilian JTF, maharba da 'Yansakai sun yi wa 'yan Boko Haram kaca-kaca a maboyarsu (Hotuna)

A wani labari mai nasaba da wannan da Legit.ng ta wallafa a daren ranar Litinin, rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Kaduna ta tabbatar da sace matafiya shidda a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuwa.

A jawabin da kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, DSP Yakubu Sabo, ya fitar, rundunar ta ce lamarin ya faru ne ranar Lahadi da daddare yayin da matafiyan ke yin bulaguro a kan babbar hanyar da ta yi kaurin suna wajen sace mutane domin yin garkuwa da su.

Labarin garkuwa da mutanen na zuwa ne a cikin kasa da sa'o'i 24 bayan rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta sanar da kashe masu garkuwa da mutane uku tare da kama wasu 25 a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna da kuma daga Kaduna zuwa Zaria.

DSP Sabo ya bayyana cewa wasu 'yan bindiga ne cikin kakin sojoji suka sace mutanen bayan sun tare wata motar fasinja da misalin karfe 11:40 na dare a daidai kauyen Rijana dake kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel