Yanzu Yanzu: Gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago za su gana a ranar 16 ga watan Satumba kan karancin albashi

Yanzu Yanzu: Gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago za su gana a ranar 16 ga watan Satumba kan karancin albashi

Gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago na kasa za su sake zama a ranar 16 ga watan Satumba, domin ci gaba da tattauna lamarin mafi karancin albashi.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta tuna cewa an dage zaman karshe da ya kamata ayi tsakanin gwamnati da kwamitin a ranar 4 ga watan Satumba.

Mista Alade Lawal, babban sakataren kungiyar JNPSN, ya tabbatar wa NAN a ranar Talata a Lagas cewa an sauya ranar zaman ne saboda uzurin jami’ai.

Kungiyar kwadago da gwamnatin tarayya dai na ta tafka rigima akan aiwatar da sabon karancin albashi wanda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya ma hannu a ranar 18 ga watan Afrilu.

Tattaunawa tsakani gwamnati da kungiyar JNPSNC, da ke wakiltan kungiyar kwadago domin yin gyara a albashin ma’aikata sakamakon sabon karancin albashin, ya hadu da cikas sakamakon rashin daidaita wasu banbance-banbance a bukatarsu.

KU KARANTA KUMA: Da duminsa: Buhari, IGP, NSA, da shugaban NIA na wata ganawar sirri a Asorock

Yayinda gwamnatin tarayya ta bukaci Karin albashi 9.5% ga ma’aikatada ke mataki na 07 zuwa 14 da kuma kari kaso 05% ga ma’aikatan da ke daga mataki na 15 zuwa 17, kungiyar kwadago na neman Karin 30% ga ma’aikata da ke mataki na 07 zuwa 14 da kuma Karin kaso 25% ga ma’aiktan da ke mataki na 15 zuwa 17.

Shugaban NLC, Ayuba Wabba ya fada ma manema labarai cewa za su goyi bayan duk matakin da JNPSN ta dauka ka karancin albashin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel