Kurungus! Kotu ta sutale gwala gwalan Diezani na $40m ta mika ma gwamnati

Kurungus! Kotu ta sutale gwala gwalan Diezani na $40m ta mika ma gwamnati

Zancen da ake yi a yanzu shi ne wata babbar kotun tarayya dake zamanta a babban birnin tarayya Abuja ta yanke hukuncin kwace wasu dimbin gwala gwalai mallakin tsohuwar ministar man fetur tare da mikasu ga gwamnatin tarayya.

Jaridar Guardian ta ruwaito Alkalin kotun, mai sharia Nicholas Oweibo ne ya yanke wannan hukunci a zaman kotun na ranar Talata, 10 ga watan Satumba sakamakon Diezani ta gagara bayyana ma kotu dalilinta na cigaba da mallakan gwala gwalan bayan EFCC ta shaida ma kotu cewa da kudaden sata aka sayesu.

KU KARANTA: Kalli ma’aikatun da gwamnan Bauchi ya tura sabbin kwamishinonin jahar guda 20

Majiyar Legit.ng ta ruwaito daga cikin gwala gwalan akwai agoguna, Sarkar wuya, awarwaro, zobba, yan kunne, sarkan kafa, wayar salula kirar iPhone, dukkaninsu na zinare, kamar yadda lauyan EFCC Rotimi Oyedepo ya bayyana.

Haka zalika cikin wata takardar rantsuwa da wani jami’in EFCC, Rufai Zaki ya mika ma kotun, ya bayyana cewa dukkanin dukiyar nan sun fi karfin sanannen halastaccen albashin Diezani, ya kara da cewa daga shekarar 2012 ta fara tattara wadannan kadarori, jim kadan bayan ta zama minista.

“Muna da dukkanin bayanan asusun bankin Diezani wanda take amsan albashi da shi, amma bata yi amfani da albashinta wajen mallakan kayan nan ba, ko kuma wani halastaccen kudinta ba, don haka muke neman kotu ta mallaka ma gwamnatin tarayya wadannan zinari.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel