Rufe wasu kan iyakoki ya jawo farashin kaya sun tashi a kasuwa

Rufe wasu kan iyakoki ya jawo farashin kaya sun tashi a kasuwa

Farashin abinci da sauran kayan masarufi sun tashi a halin yanzu bayan an rufe wasu daga cikin kan iyakokin Najeriya na wani lokaci. Wani bincike da Daily Trust ta yi ya tabbatar da wannan.

Masu shigo da kaya daga kasashen ketare da ke makwabataka da Najeriya sun kara kudin bayan wani rufe bakin iyakokin kasar da aka yi. Ofishin NSA ta bada shawarar daukan wannan mataki.

Kayan da ake shigowa da su sun fara wahala, sannan farashi ya tashi sama kamar yadda rahotanni su ka nuna. Sai dai an kuma gano cewa man da ake sha a fadin kasar ya ragu sosai.

Amma a Kauyukan da ke gab da wajen Najeriya a jihar Ogun, har ta kai ana saida litar fetur a kan N350, a maimakon N145 da gwamnati ta kayyade. Ana samun irin wannan matsala a jihar Kwara.

Buhun shinkafa da bai wuce N13, 000 zuwa N15, 000 a baya, ya dawo N16, 000 zuwa N20, 000 yanzu. A yankin Adamawa da ke makwabtaka da kasar Kamaru, har ta kai kudin burodi ya tashi.

KU KARANTA: Ba za a iya dakatar da harin da ake kai wa bakin haure a Afrika ta Kudu ba

A karshen Arewa maso Gabashin kasar inda aka saba fita da kayan marmari irinsu lemu zuwa ketare, rufe iyakokin ya jawo farashin lemu sun karye a gida bayan fita zuwa Kamaru ya yi wuya.

Wani abin mamaki kuma shi ne wannan mataki da gwamnati ta dauka ya jawo ana fasa kauri ta cikin ruwa. A yankin Legas a na shigo da kaya a boye ta kogi yayin da farashin kaya su ka mike.

A daidai wannan lokaci kuma Manoma sun fadawa Manema labarai cewa masara ta fara tsada a wasu jihohin Arewacin Najeriya. Hakan na zuwa ne bayan shinkafa na neman ta gagari mutane.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel