Jam'iyyar APC ta dau alwashin daukaka kara akan nasarar da kotu ta baiwa Ekweremadu

Jam'iyyar APC ta dau alwashin daukaka kara akan nasarar da kotu ta baiwa Ekweremadu

- Jam'iyyar APC ta dau alwashin daukaka kara sakamakon nasarar da kotu ta baiwa Ekweremadu

- Shugaban jam'iyyar APC na jihar Enugu, Ben Nwoye ne ya sanarwa manema labarai hakan

- Shugaban ya kara da jinjinawa lauyoyin masu kara inda ya ce sun yi kokari

Jam'iyyar APC ta ce zata daukaka kara akan nasarar tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa da kotu ta tabbatar.

Shugaban jam'iyyar APC na jihar Enugu, Ben Nwoye, a tattaunawar da yayi da kamfanin dillancin labarai akan hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe ta yanke ne ya tabbatar da hakan.

'Yar takarar kujerar sanata ta yankin yammacin Enugu, Juliet Ibekaku-Nwaguwu ta jam'iyyar APC ta tunkari kotun sauraron kararrakin zaben da korafi bayan an bayyana Ekwerwmadu a matsayin wanda ya lashe zaben.

KU KARANTA: Kamfanin jiragen sama na British Airways ya soke tashin daruruwan jiragen sama

A hukuncin da kotun ta yanke a ranar 9 ga watan Satumba, 2019, ta sallami karar ne sakamkin rashin shaidun da zasu tabbatar da rashin nasarar Ekweremadu.

Nwoye yace sun bi duk yadda ya dace don daukaka karar.

Yace jam'iyyar ba ta gamsu da hukuncin kotun ba saboda ta mika duk shaidun da ake bukata don tabbatar da zarginta.

"Munyi mamakin yadda hukuncin ya kasance duk da shaidun da muka gabatar," inji shi.

Nwoye yayi jinjina ga lauyoyin masu korafin don sunyi kokari a kotun.

Patrick Luke, lauyan masu kara, yace masu karar sun umarcesa da ya daukaka kara.

"Akwai kura-kurai a hukuncin. Zamu nazarcesu sannan mu maida martani."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel