Da duminsa: Buhari, IGP, NSA, da shugaban NIA na wata ganawar sirri a Asorock

Da duminsa: Buhari, IGP, NSA, da shugaban NIA na wata ganawar sirri a Asorock

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya shiga wata ganawar sirri da shugabannin hukumomin tsaron Najeriya a fadarsa ta Asorock dake birnin tarayya, Abuja.

A wurin ganawar akwai babban sifeton rundunar 'yan sanda na kasa (IGP), Mohammed Adamu, mai bawa shugaban kasa shawara a bangaren tsaro (NSA), Babagana Monguno, da shugaban hukumar tsaro ta sirri (NIA), Ahmed Rufa'i Abubakar.

Wata majiyar fadar shugaban kasa ta ce ganawar ba zata rasa nasaba da matsalolin tsaron cikin gida da ake fama da su da kuma hare-haren da ake kai wa 'yan Najeriya a kasar Afrika ta Kudu.

Shugaban hukumar tsaro ta NIA, wanda Buhari ya wakilta zuwa kasar Afrika ta Kudu a kan harin da ake kai wa 'yan Najeriya, ya mika rahotonsa ga shugaban kasa.

DUBA WANNAN: Majalisar wakilai ta aika sammaci ga wasu manyan hadiman gwamnatin Buhari guda uku

Taron na zuwa ne a daidai lokacin da satar mutane tare da yin garkuwa da su ke neman dawowa kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.

A ranar Litinin ne ministar tsaron kasar Afrika ta Kudu, Uwargida Mapisa Nqakula, ta bayyana cewa gwamnatin kasar ba zata dakatar da hare-haren da ake kai wa bakin haure ba.

Tuni shugaba Buhari ya bayar da umarnin fara kwaso 'yan Najeriya daga kasar Afrika ta Kudu domin dawo da su gida.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel