Sanatar Legas Oluremi Tinubu ta samu nasara a kotun zaben 2019

Sanatar Legas Oluremi Tinubu ta samu nasara a kotun zaben 2019

Kotun da ke sauraron karar zaben majalisar tarayya da jihohi na 2019 a jihar Legas ta yanke hukunci a game da korafin da ake yi a kan nasarar da Sanatar APC Oluremi Tinubu ta samu.

A zaman karshen da kotun da ke sauraron korafin zabe ta yi a Ikeja, Alkalai sun yi watsi da karar da aka shigar a kan Sanata Oluremi Tinubu mai wakiltar tsakiyar Legas a majalisar dattawa.

Kamar yadda rahotanni su ka zo mana daga jaridar This Day, bayan kimanin sa’a bakwai ana karanto hukunci a kotu, Alkali mai shari’a Kunaza Hamidu, ya yi fatali da karar da PDP ta shigar.

Kotu ta bayyana cewa ‘dan takarar jam’iyyar PDP a zaben na 2019 watau Adesunbo Onitiri, bai iya gamsar da ita da hujjojin da za su sa a soke nasarar da hukumar INEC ta ba Sanata mai-ci ba.

Manyan Alkalai W.R. Olamide da S.I. Okpara ne su ka taimakawa babban Alkali Kunaza Hamidu wajen yanke wannan hukunci. Alkalan sun tabbatar da cewa APC ta ci zabe a Legas ta tsakiya.

KU KARANTA: 'Dan Majalisar Jihar Kaduna mai-ci ya samu nasara a kotu

Kotu ta ce babu hujjoji a korafin da aka kawo gabanta ana kalubalantar nasarar da Sanata Oluremi Tinubu ta samu a zaben Fubrairun 2019. Wannan ya sa aka tabbatar da matakin INEC na farko.

A zaben da aka yi, INEC ta bada sakamakon cewa Tinubu ta samu kuri’u 131. 735 ne inda ta doke babban Abokin takararta na PDP, Mista Onititi. ‘Dan takarar na PDP ya tashi ne da kuri’a 89 107.

PDP ta shigar da kara kotu ta hannun Lauya Onome Akpeneye bayan an bayyana sakamakon zaben. ‘Dan takarar PDP wanda ya zo na biyu yana ikirarin INEC ta yi kuskure a zaben da aka yi.

Ezekiel Ashade da Busayo Onabanjo su ne Lauyoyin da su ka tsayawa Tinubu, APC da hukumar INEC a shari’ar inda su ka nunawa kotu cewa babu inda aka yi amfani da kudi wajen magudi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel